Godiya ta tabbata ga Allah Mai juya watanni Mai kaddara al’amura, Mai shigar da dare cikin rana Ya shigar da rana cikin dare. Ya sanya wa komai iyaka kuma Ya saka wa kowane aiki da sakamako, Ya sanya duniya gona ce don gobe Lahira a girbe abin da aka shuka, kuma Ya sanya duniya kasuwa ce da bayin allah suke sayen guzurin Lahira. Madalla da wanda ya sayi kyakkyawan guzuri, tir da wanda ya lalata rayuwarsa ya manta da Ranar Sakamako.
Ina gode wa Allah a kan ni’imar da Ya yi mana ta sarari da ta boye. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma Annabi Muhammad (SAW) Manzon Allah ne kuma bawan Allah ne.
Bayan haka ya ku mutane! Mu yi guzuri hakika mafificin guzuri shi ne tsoron Allah, ga shi shekara tana neman karewa, kuma ga shi an rage mana kwana 355 ba za su dawo ba. Abin kawai da ya rage shi ne abin da muka aikata a cikinsa alheri ne ko sharri. Haka kowane kwanan rayuwa, zango-zango, rana bayan rana, mako bayan mako, shekara bayan shekara da haka iya kawanakin da Allah Ya diba mana a duniya za su kare.
Allah Yana cewa “Ranar Kiyama, rana ce da kowane rai zai samu abin da ya aikata na alheri ko na sharri ga shi nan a sarari. Sai rai ya ce “Ina ma da tsakanina da wannan aiki kamar nisan sama da kasa ne.”
“Ku tuna ranar da kowane rai zai samu abin da ya aikata na alheri ko sharri, kuma da abin da ya aikata na barna. Rai zai rika burin ina ma a ce za a samu rata mai yawa tsakaninsa da shi.” (Suratul Ali-imran aya ta 30).
Sabuwar Shekara
“Hakika adadin watanni a wurin Allah wata goma sha biyu ne acikin Littafin Allah, tun ranar da aka halicci sammai da kasa, daga cikinsu akwai wata hudu masu alfarma. Wannan shi ne addini madaidaici…” (Suratul Tauba aya ta 36).
Wannan ayar tana nuna yawan watannin da ke cikin shekara ne, wato goma sha biyu kuma haka Allah Ya tabbatar a Lauhul Mahfuz sannan daga cikin wadannan watanni akwai guda hudu da aka haramta yin yaki ko ta’addanci a cikinsu, saboda alfarmarsu. Watannin kuwa su ne; Zul-Kida da Zul-Hajji da Muharram da kuma Rajab. Ukun farko da muka ambata a jere suke, na karshe wato Rajab shi ne kawai a ware.
Don haka yanzu ga shi sabuwar shekara tana daf da shigowa, abin da ya kamata mu yi shi ne mu yi wa kanmu hisabi saboda an samu Hadisi Sayyidina Umar (RA) ya ce “Ku yi wa kanku hisabi kafin ranar da za a auna ayyukanku.” Kuma Annabi (SAW) ya ce “Mai hangen nesa shi ne wanda ya yi wa kansa hisabi kuma ya yi aiki da shi.” Kuma Annabi (SAW) ya sake cewa “Ranar Kiyama ba wani bata lokaci za a yi ba saboda kowa ayyukansa an auna su. Don haka wanda ya samu alheri sai ya gode wa Allah, wanda kuma ya samu akasin haka, to kada ya zargi kowa ya zargi kansa.
Ga shi zamu shigo sabuwar shekara ta hijra ta 1441. Watanni a wajen Allah wata goma sha biyu ne ga su nan kamar haka:
- Al-Muharram
- Safar
- Rabi’ul Awwal
- Rabi’us Sani
- Jimada Ula
- Jimada Sani
- Rajab
- Sha’aban
- Ramadan
- Shawwal
- Zul- Kida
- Zul-Hajji.
Wadannan su ne watannin Musulunci, kuma su ne watannin hijra. Sayyidina Umar (RA) ya tambayi sahabbai wane lokaci ya kamata ya zamar mana farkon lissafin watannin Musulunci, sai sahabbai suka ba shi shawarwari guda uku;
- Wadansu suka ce a fara daga haihuwar Annabi (SAW).
- Wadansu suka ce a fara daga ranar da Annabi (SAW) ya fara samun wahayi.
- Wadansu suka ce a fara daga ranar da Annabi (SAW) ya dawo Madinah.
To a nan sai Sayyidina Umar (RA) ya zabi sharawa ta karshe. Sai aka sanya ta ta zama farkon lissafin watanninmu na Musulunci daga Hijrar Annabi (SAW) daga Makka zuwa Madina.
Don haka yanzu idan za mu yi lissafi a shekara ta Musulunci sai mu ce yau 24 ga watan Zul-Kida shekara ta 1440 alal misali wadda ta yi daidai da 27 ga watan Yuli 2019, Miladiyya.
Don hakane nasiha ta farko muna jawo hankalin mutane su rika sanya watannin hijra a rubuce-rubucensu suna hadawa da watan ’yan albashi, kamar yadda wannan jarida mai daraja da alheri Aminiya take yi. Wato idan muka zo rubuta wasika ko takadar sanar da daurin aure ko wani taro. Wannan zai sa mu rika tuna wa junanmu muhimmancin kwanakin watan Musulunci.
Wannan makala za mu tattauna ne a kan watan daya da muhimmancinsa a kan Musulmi shi ne;
Al-Muharram: An samu Hadisi daga Abu Huraira (RA) daga Manzon Allah (SAW) ya ce “Bayan azumin Watan Ramadan shi ne watan Allah da kuke kira Al-Muharram. Fiyayyiyar Sallah ita ce nafilfilin dare. Mutum biyar suka ruwaito ban da Buhari.
Aliyu (RA) ya ce wani mutum ya zo ya tambayi Annabi (SAW) cewa wani wata ne ka umarce ni in rika yin azumi bayan watan Ramadan? Sai Annabi (SAW) ya ce “Idan ka yi azumin bayan watan Ramadan to ka yi azumin watan Al-Muharram domin shi ne watan da Allah Yake karban tubar masu tuba sannan Yake yafe wasu zunubai masu zuwa.” Imam Tirmizi ya ruwaito.
Azumin Ashura
Yanzu za mu yi magana ne a kan Azumin Ashura. Rana ce ta nasara mai girma don rana ce da Allah Ya hallaka Fir’auna Ya tserar da Annabi Musa (AS). Don haka ga yadda labarin yake:
“Jayayya da rigima kullum na nan tsakanin karya da gaskiya, haka kuma tsakanin masoyan Allah da kuma masoyan Shaidan. Wadanda suka ba da gaskiya suna yaki ne saboda Allah, wadanda kuma suka kafirta suna yaki ne saboda Shaidan. To ku yaki iyalin Shaidan. Hakika makircin Shaidan mai rauni ne.” Da Allah Ya ga dama zai kawar da karya ce sai gaskiya ne kawai za ta tabbata amma Allah bai yi haka ba, sai Ya bar karya da gaskiya don a jarrabi wadansu mutane a kan wadansu. Ya ce; da ya ga dama da ya hallaka azzalumai amma sai ya ba su ya sanya bayinsa muminai don ya jarraba su don a gane kiyayyar kafirai.
Hakika Allah Ya ba da labarai da yawa na rigima da ke tsakanin muminai da kafirai. A cikinsu akwai kissar Annabi Musa (AS) tare da Fir’aunan Masar. A zamaninsu kuma Allah Ya yi ta nanata tarihinsu a cikin Alkur’ani a kusan wurare 30 a bigire daban-daban. Ita ce ma ta fi yawan nanatawa a cikin kissosin Alkur’ani. Dalili kuwa saboda wahalar da Annabi (SAW) ya sha wurin Kuraishawa ta yi daidai da irin wahalar da Annabi Musa (AS) ya sha a wajen Fir’auna, don ta zaman masa hukuntarwa da ba da hakuri gare shi da kuma muminai. Abin da ya sa aka yi ta nanata kissar saboda tana tare da wa’azi mai dauke da darussa da hujjoji da ayoyi na yanke shakku a cikinsu.
Za a iya tuntubar SP Imam Ahmad Adam Kutubi ta 08036095723