✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maraba da Ramadana a shekarar 1434BH

Ya ku wadanda ku ka bada gaskiya, an wajabta azumi akan ku, kamar yadda aka wajabta akan wadanda suka gabace ku (an yi haka ne),…

Ya ku wadanda ku ka bada gaskiya, an wajabta azumi akan ku, kamar yadda aka wajabta akan wadanda suka gabace ku (an yi haka ne), don ku ji tsoron Allah 2:183. Allahu Akbar, kwanci-tashi ba wuya wurin Allah, ga shi kamar jiya a daidai irin wannan lokaci dukkan al’ummar Musulmin duniya muke ta addu’ar Allah Ya nuna mana shigowar watan azumin shekarar 1434BH, yau kuma ga shi muna begen ganin wanda za a fara tsakaninn gobe da jibi, in Allah Ya so, a zaman azumin shekarar 1435BH. Allah Don girman zatinKa da IzzarKa da daukakarKa, Ka nuna mana na bana, kuma Ka sa idan mun yi mu rabauta da dukkan tanade-tanaden da Ka yi alkawarin bai wa wanda ya yi ingantaccen azumin watan na Ramadan, wato gafara da kuma samun shiga AljannarKa Firdausi, amin summa amin.
Shi dai Azumin watan Ramadan yana daga cikin shika-shikan Musulunci guda biyar, sauran hudun sun hada da fadin Kalmatu shahada da kudurtar abin da ta kunsa, na ba wanda ya cancanci a bauta masa, sai Allah SWT, da kuma yin imani da Annabi Muhammadu SAW, Manzon Allah ne, kuma shi ne Annabin karshe, kuma cikamakon Annabawan Allah, sai tsayar da sallah kamar yadda sunnah Manzo SAW, ta koyar da ziyartar dakin Allah SWT da ke birnin Makkah, wato aikin Hajji, ga wanda Allah Ya ya samu iko, kamar na lafiyar jiki da ta hanya da guzuri, da sauran tanade-tanade da shari’ah ta yi.
Hausawa kan ce Azumi  garkuwar Musulmi, ina jin ba don kome suke fadin haka ba, sai don irin tanade-tanden da suka wajaba mai azumi ya kasance da zarar yana azumi da kuma irin rahama da gafara da ceto da ake da su a cikin watan gaba dayansa, sa’anin a sauran watanni 11,, ta yadda a sauran watannin za ka ji ana batun ke’e wasu kwanaki a cikinsu a bayyana falalarsu. Alal misali kwanaki 10, na watan Zul Hijjah da kwanaki 9 da 10, na Tasu’a da Ashura da ke cikin watan Muharram da daren Juma’a da makamanta kwanaki ko yini. Shi watan Azumi gaba dayansa, ba shi da gefe cikin samun kar’ar ayyukan alheri  dare ba rana, watan da a cikinsa ake bude kofofin Aljanna, a kuma rufe kofofin wuta, sannan a daure Shedanu.
Don haka azumin watan Ramadan lokaci ne da ake bukatar musulmi ya daidaita tsakaninsa da Mahaliccinsa, bisa ga kura-kuran da yake aikatawa, da kuma neman kara kusantar Allah da neman taimakonSa da kariyarSa, musamman na irin halin da mu Musulmi muke ciki yanzu anan kasar na rigingimu da kashe-kashe irin na ‘yan kungiyar Boko Haram da na Fulani makiya da manoma da batun fashi da makami da yin garkuwa da mutane da rashin mulkin adalci irin na shugabanni da annoba irin na fyade da cin hanci da rashawa da talaucin da ya mamaye mu da irin kaskancin da yanzu Musulmi a Arewacin kasar nan muke gani a gida da dawa..
Don haka akwai bukatar a wannan azumi mu kara kyautata tsakaninmu da Allah SWT da kuma tsakaninmu da iyalenmu da ‘yan uwanmu da makwabtan na gida da  na kasuwa ko ofis, ba tare da nuna bambancin addini ko harshe ko yare ko jinsi da makamantan bambance-bambancen da muke nunawa karara ba, alhali Allah Ya sa mana wadannan bambance-bambance ne kawai don mu san junanmu, amma ba don kiyayya ba. A takaice dai kowane Musulmi ya yi kokarin daina mummunan ayyukan da yake aikatawa a cikin rayuwa, zuwa aikata ayyukan alheri da kuma kudurtar aniyar zai ci gaba da yin hakan koda kuwa azumi ya wuce, wadannan su ne matakan zaman mu lafiya tsakanin mu da Allah da kuma a junanmu,  don neman karuwar arziki da ci gaban kasar mu da ma na duniya baki daya.
Ba wai hana kai ci da sha da yin jima’i da rana ba ne kawai yin azumi ba, a’a, lallai rai da gangar jiki da zuciya ana bukatar saitasu akan ayyukan alheri a lokacin azumi da nisantasu daga dukkan wata yashashshiyar magana ko aiki, ba kuma wani musu koda kuwa na raha ne, kamar yadda Hadisin Manzo SWA da aka ruwaito daga Abu Huraira RA ya ce: “Azumi garkuwa ne gareku, don haka idan kana yin azumi, ka zama mai kame kai da kiyaye harshenka wajen yin zancen banza, ta yadda idan da wani zai zage ka, sai ka ce da shi Ni ina azumi! Ni ina azumi!!”
Saboda girma da falalar ibadar watan azumi, Allah (SWT) Ya ke cewa kowace ibada ta dan Adam ce, amma azumi nasa Ne, Shi kadai zai saka wa bawa, saboda sirrin da ke tsakaninSa da mai yinsa, wato ma’ana mai azumi ka iya shiga daki ya ci ya sha, ya kuma fito bainar jama’a ya ce yana azumi ba wanda zai musanta masa, amma saboda imani da ya yi, na ya yi azumin ya sanya ya kauce ma yin haka. Allah Ya sa mu da ce.
To tunda ga irin rahama da falala da albarkar da ke tattare da ibadar watan azumi, wanda a cikinsa kadai ake dacewa da daren Lailatin kadari, wanda Allah (SWT) ke cewa ya fi ibadar dare dubu, (sama da shekaru 83), shekarun da ba kowane mutum ke cimmasu a rayuwa ba, imma ya kai din, za ka tarar ba cikakkiyar lafiya, bare ya samu tsayar da ibada yadda ya kamata. Da wannan ke nan ba abin da ya fi alheri ga dukkan Musulmin da Allah Ka rabautar da shi wajen ganin wannan muhimman lokaci, da ya wuce mutum ya dukufa da yin ayyukan alheri, kamar ziyartar wuraren da ake tafsiri da sauran karantarwar addinin Islama da kokarin kara yin nafilfili da yawaita kyauta da sadaka da sada zumunci da ciyarwa da dukkan wasu ayyuka da za su kara daga darajarsa wajen Allah a wannan muhimmin lokaci mai tsada. Allah Ka rabautar da mu wajen ganin wannan wata da yin ibada karbabbiya, amin summa amin. Maraba da azumin watan Ramadan.