✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manyan Gobe barka da warhaka 03

Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Mai tallar nono. Labarin na gargadin a guji…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya, Allah Ya sa haka amin. A yau na kawo muku labarin Mai tallar nono. Labarin na gargadin a guji dogon buri a rayuwa.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Mai tallar nono

An yi wata mai tallar nono a wani kauye. Rannan sai ta je ruga ta tatsi nonon shanu domin ta sayar; ba ta bar rugar ba har sai da ta cika babbar kwaryarta da nono.
Tana dawowa gida sai ta fara tunanin irin abubuwan da za ta yi da nono bayan ta sayar, “Yanzu zan cire man shanu, na yi cikwi, sannan zan sayar da sauran nonon. Idan na samu kudi zan sa yi kaji, idan kajin sun yi kwai zan sayar na sayi gona.”
Cike da farin ciki ta ci gaba da cewa “idan kajin suka yi ‘ya’ya zan sayar da su na sayi riga mai kyawun da idan na sanya duk saurayin da ke kauyen sai ya kalle ni, inda zan rika taku ba tare da tanka musu ba.”
Tana cikin wannan burin har ta manta cewa tana dauke da kwaryar nono a kan ta. Juyawar da za ta yi irin ta rangwada, sai kwaryar ta fado ta fashe nonon ya zube gaba daya!
Sai ta kwalla ihu “wayyo Allah yaya zan yi duk shirina ya rushe?”
Ina son Manyan Gobe su guji dogon buri, su gane duk abin da Allah Ya nufa za su samu, to babu makawa ba zai tsallake su ba, shi ya sa ake cewa rabon kwado ba ya hawa sama.