✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manya ku yi kokarin ceto Arewa

Hakika Arewacin Najeriya na cikin wani mummunar hali, wanda ya kamata duk wani mai kishin yanki  da al’ummar yanki ya yi wani yunkuri dan ceto…

Hakika Arewacin Najeriya na cikin wani mummunar hali, wanda ya kamata duk wani mai kishin yanki  da al’ummar yanki ya yi wani yunkuri dan ceto yanki daga halin da yake ciki. Na san wasu za su ce mai yasa ban ware wani bangare na al’ummar Arewa na rubuta masu wannan wasika ba na rubuta ga duk jama’ar Arewa, misali na rubuta ga Dattawan ko Gwamnonin ko Sarakunan Arewa, to dalili shi ne duk wani mai kishin Arewa akwai rawar da ya kamata ya taka don ceto wannan yankinmu daga ciki kunci da mugun hali da makiyanmu suka jefa mu.
Yanzu a ce mu ke da Yakubu Gawon da Shehu Aliyu Shagari da Janaral Muhammadu Buhari da Ibrahim Badamasi Babangida da Abdulsam Abubakar, amma a ce yankin mu ya shiga matsala, ku tuna fa kun yi mulkin Najeriya, kuma kun san duk wata matsalar Najeriya ciki da bai, kuna da bayanan shirri na tsaron, amma kun yi shiru kullum yankin nan kara fadawa cikin rikici yake yi. To haka za ku zura ido har sai Arewa ta zama tarihi?
Ga dan uwanku daya daga cikin tsofaffin shugabanni biyu da Kudancin Najeriya ke da su, wato Obasanjo ya fito ya rubuta wasika mai shafi 18, wadda a ciki ya bayyana cewa za a kashe mutum dubu masu tasiri a Najeriya kafin zaben 2015, amma kuma kun kasa yin komai akan wannan wasika shin kuna jira har sai Jonathon ya aiwatar da abin da Obasanjo ya ce zai aiwata kafin 2015? yanzu bakwa ganin wannan wasikar ta Obasanjo a matsayin abin kunya a kanku? Sannan ina so ku sani cewa, idan kuna ganin don wannan tashin hankalin bai tabaku ba, don haka kuka yi shiru, to fa a kwana a tashi zai zo kanku, kuma abin da ya faru da daya daga cikinku a Kaduna ya isheku ishara, wato Janar Buhari, to wai ma kuna ina Azazi yana Mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkar tsaro ya fito ya ce babu Boko Haram, PDP ce. Kun sani cewa yasan harkar tsaro ce tasa aka ba shi wannan mukami, amma kun yi shiru ana ta kashemu da sunan wannan kungiya? Ya kamata ku fidda duk wani bambanci da ke tsakaninku ku samo wa yankinku mafita.
Gwamnonin Arewa, gaskiya kun ba ni kunya a ce wai kun kasa haduwa ku fitar da wata sahishiyar hanya da za ku yaki matsalar tsaro a tare, sai dai kowa ya yi nasa? Idan wannan ya yi Gabas, wannan ya yi Yamma! Duk da na san ba kuke da ‘yan sanda ba ko Sojoji, amma nasan kuna da fada aji kan harkoki tsaro a Jihohinku, don haka ya kamata ku hadu ku ajiye bambancin jam’iyya ku samo wa yankinnan mafita.
Sarakunan Iyayen al’umma, sarakunan Arewa wannan sunan naku na iyayen al’umma yana neman zaman tarihi, domin duk iyaye nagari bai kamata suna ganin ‘ya’yansu sun shiga matsala ba, su zura ido; kuna gani fa Allah ya jikan rai, Allah ya gafarta wa Mai martaba Alhaji Ado Bayero, yadda aka kai masa hari ban da Allah ya kare shi, da tun lokacin ya rasa ransa. Haka sarakunan uku a  Maiduguri da suka hada da Sarkin Goza da Askira da Uba da za su gaisuwa Gwombe, aka kai masu hari. Idan har aka kashe sarkin Goza. Amma kuma kun yi shiru kun san kuna da kima a idanu jama’a da kuma masu mulkin Najeriya, amma kuka je fadar Shugaban kasa, shan ruwa kuka kasa yi masa magana akan irin tashin hankali da Arewa ke ciki.
kungiyar Dattawa Arewa, ya kamata wannan kungiya ta fitar da wani tsari wanda zai yi hasashen ci gaban da Arewacin Najeriya zai samu nan da shekaru ashin 20 ko ma fiye da hanyoyin da za a bi don cimma hakan, a kuma tabbatar ana amfani tsarin da zai kunshi tattalin arziki da zamantakewa.
Malaman addini kuma kuna da rawar takawa a kan wannan masifa da ke damun wannan yanki, ku tuna ku ne magada Annabawa, ku ne kuke koyar da ilimantar da tunatar da al’umma, to ya kamata ku rika dora al’umma akan koyarwar Alkur’ani da hadisan manzo Allah (S.A.W), ku dubi hakki da yake kanku, amma wasunku ne ke sa masu neman mulki yin zina da luwadi akan cewar idan sun yi haka, za su samu mulki, kun mata Allah ke bayarwa? Ya kamata ku dawo kan tafarki madaidaici, ku daina fassara aya bisa son rai don ta yi wa wani dadi. Kuma ku rika fadin gaskiya komai dacinta.
‘Yan jarida ku sani kuke da hakkin bayyana wa al’umma gaskiyar abin da ke faruwa, kalma daya za ku fada ta jawo tashin hankali, har ya zama ta iya jawo yaki. Don haka sai kun yi taka tsan-tsan wajen aikinku, kuna da hakki binciko gaskiyar al’amari, domin bayyana wa al’umma, amma sau da yawa bakwa yin haka, akan kai hari a wasu wurare sai ku dogara da hukumar ‘yan sanda, ku dora wa wata al’umma ko kungiya nauyin kai hari. Misali an kai hare-hare a wasu kauyuka na Katsina da Zamfara, amma sai kuka ce Fulani ne wanda idan aka dubi irin makaman da aka yi amfani da su, an san sam Fulani ba za su iya malakar su ba, haka wani lokacin idan an kai hari sai kuce ‘yan Boko Haram ne, amma da an yi sa’ar kama masu hannu a kai hari sai a ga kiristoci ne, to mai ya hada kirista da boko haram? Dan haka sai kun kara kwazo wajen binciko anishin al’amari.
Talaka bawan Allah, hakika talakawa ma nada rawar takawa, domin kubutar da wannan yanki daga matsala, ku sani cewa iyayenmu ne talakawa suka kori Turawa ‘yan mulki mallaka, suka bai wa Najeriya ‘yancin kai a 1960, haka dai talakawa ne suka kori sojoji daga mulkin Najeriya suka mika wa farar hula mulki a 1999, Don haka a yanzu ma idan har talakawa suka fito suka jajirce, to za mu kori azzaluman shugabanni a Najeriya. Ku sani babu wanda ya gagari naki duk shugaban da zai zaluncemu idan muka ce mun ki dole ya hakura, kuma za mu ce mun ki ta hanya biyu: Ta farko idan an zo zabe mu juya masa baya, idan ya yi magudin zabe ya ci, to mu fito tituna, ko mu samu fili mu yi zaman dirshan ba gudu, ba ja da baya, sai ya ajiye ya gudu da kafarsa, tunda muna ganin abin da yake faruwa a kasashen duniya, inda talakawa ke jajircewa sai sun canza azzaluman shugabani, munga abinda ya farua Tunusiya da Masar.
Jami’an tsaro, ku ne ake amfani da ku wajen hana mu mu bayyana ra’ayinmu a duk lokacin da hukumomi suka yi mana ba daidai ba, ku ne kuke hana mu zanga-zanga a duk lokacin da aka yi abin da bai yi mana dadi ba, amma fa ku duba rayukanku rikicin nan ya fi lakumewa tun daga faruwarsa har zuwa yanzu, inda har ta kai ku da za ku kare rayuwa da dukiyar al’umma, amma kun koma kare rayuwarku da ta masu mulki, al’umma kuwa ko oho! Ya kamata a duk lokacin da jama’a suka fito zanga-zanga, to ku ba su tsaro kuma ku tabbatar ba su lalata kayan gwamnati ba.
Ina da karfin gwiwar cewa Arewacin Najeriya zai dawo hayyacinsa na zaman lafiya har tattalin arziki ya bunkasa, amma fa sai mun tashi tsaye kowa ya taka rawar da ya kamata ya taka. Allah ya ba mu ikon gyara halayenmu, ya kuma ba mu rinjaye a kan makiyanmu. Amin.

Balarabe Yusif Babale Gajida, Shugaban kungiyar Muryar Talaka Reshen Jihar Kano. 08036318846; [email protected].