✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manufarmu inganta karatu da rubutu – Shugabar kungiyar marubuta ta ‘Mace Mutum’

Shugabar kungiyar mata marubuta ta ‘Mace Mutum,’ Malama Rahma Abdulmajid ta bayyana cewa sun kafa kungiyar ne da nufin bunkasa harkokin karatu da rubutu a…

Shugabar kungiyar mata marubuta ta ‘Mace Mutum,’ Malama Rahma Abdulmajid ta bayyana cewa sun kafa kungiyar ne da nufin bunkasa harkokin karatu da rubutu a cikin al’umma.
A wata takarda da ta aiko wa filin Adabi na jaridar Aminiya, shugabar ta lissafo wasu daga cikin manufofin kafa kungiyar, kamar haka:
“Inganta rubutun mata da fadada kasuwancin littattafansu. Hada hannu da al’umma da kuma hukumar da ta dace don gyara tarbiya, zamantakewa da dawo da doka ta hanyar adabi. Dawo da martabar rubutu, marubuta da karatu a makarantun ilimi. daga martabar addini da al’adu da yakar munanan bakin al’adu a cikin adabinmu. Farfado da dabi’ar karance-karance a zukatan al’umma. Samar da gidauniyar ayyukan jinkai, tallafi da yabon gwani.”
kungiyar ta ‘Mace Mutum’ wacce aka kafa watanni uku da suka gabata, ko wadanne nasarori ta samu a zuwa yanzu? Shugaba Rahma ta bayyana nasarori 15, wadanda suka hada da:
“kungiyar ta yi rijista a matsayin kungiya mai zaman kanta (NGO) da za ta iya gudanar da ayyukanta a kowane sashi na duniya. Ta kafa shugabanni daga gida har kasashen waje, kamar su jamhuriyar Nijar da sauransu. Ta samar da kayan aiki na zamani da kowace kungiya ke bukata. Ta sami membobi sama da dari, inda ta kammala yi wa akalla arba’in daga cikinsu rijista.”
Sauran nasarorin, a ta bakin Malama Rahma; sun hada da: “kirkiro da sabon salon rijistar ’ya’yan kungiyar, ta hanyar buga littafin kundin dokokinta a cikin ingataccen bugu, inda za a hada wa memba da fom don ya duba ya ga tsarinta kafin ya cike; don sanin zai iya ko ba zai iya ba, sannan a ba shi katin shaida. Ta samar da turaku a Facebook, musamman don yada kanta. Sannan ta samar da turke na kowa da kowa da kuma wani na daban, domin ’ya’yanta masu rijista kawai da kuma wani na shugabanninta.”
Cikin nasarorin kungiyar, har da: “Tsara karatun kara wa juna sani a duk Litinin, inda ake koyar da dabarun rubuta littafi mai ma’ana da ingancin aiki da samar da sabbin jigogi. kungiyar ta samar da tsarin yin labarun hada-ka na gamayyar gajerun labaru kan sabbin jigo tsakanin ’ya’yanta, kazalika sabbin tatsuniyoyi da zaben wasu zaratan ’ya’yanta guda uku don samar da wasu littattafai uku na dogon labari cikin sabbin jigo; karkashin tsangayar ‘Gudaji Panel.’
“Tana tattara ayyukan bita da kara wa juna sani don mayar da shi littafi ga marubuta mata da ba su cikin Facebook. Ta samar da iyaye da mashawarta da abokan hulda, inda ta tsara takardu da ake zuwa ziyarar ban girma ga wadanda suka dace su santa. Ta samar da tsari na musamman na kare ayyukan ’ya’yanta daga barayin zaune, masu satar fasaha. kulla yarjejeniya da Hukumar dakunan Karatu Ta kasa, don samar wa ’ya’yanta lambar ISBN cikin hanzari da rahusa.
“Ta samar da tsari na zamowa kungiya ta farko da za ta fara cin kasuwar yanar gizo, inda ta kera shago na yanar gizo don sayar da littattafai, wanda zai fara aiki nan ba da dadewa ba. Hankoron fadada kasuwancin littafi daga inda yake a Arewacin Najeriya zuwa fadin duniya, inda take aikin tuntuba tukuru, tsakaninta da diloli da manzannin aike a duniya. Haka kuma, ita ce kungiyar mata Hausawa ta farko da ta samar da dabarun da ka iya yakar gulma da tsegunguma, don tabbatar da an mayar da hankali ga aiki; inda take leken asiri ga masu irin wannan hali da kuma bayar da horo mai tsanani ga wanda aka kama da laifi.”
Wasu daga cikin marubuta kuma ’ya’yan kungiyar, sun hada da Bilkisu Yusuf Ali, Asma’u Lamido, Sadiya Garba, Sa’adatu Baba Ahmed, Lubabatu Ya’u da sauransu da dama.