✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Manoman shinkafa da suka yi asara na bukatar tallafi —RIFAN

Ta bukaci ta taimaka wa manaoman shinkafa da suka yi asara sakamakon ambaliya a Jihar Kano

Manoman shinkafa a Jihar Kano sun nemi Gwamnatin Tarayya ta tallafa wa ’ya’yanta lura da dimbin hasarar da suka tafka sakamakon ambaliyar ruwa da ta tafi da amfanin gonarsu.

Wannan kira ya fito ne daga Ma’ajin Kungiyar Manoman Shinkafa ta Kasa (RIFAN) reshen jihar Malam Shu’aibu Husaini a lokacin zagayen auna gonakin da ambaliyar ta shafa a kananan hukumomin Wudil da Garko da ke Jihar Kano.

Ya ce manoman da suke kananan hukumomi, ambaliyar ta cinye musu amfani don haka akwai bukatar gwamnati ta kawo musu dauki na musamman.

“Mun ga yadda gonaki masu yawa suka auka cikin wannan bala’i, ruwa ya tafi da duk shinkafar da suka noma.

“Lamarin akwai ban tausayi, ’yan kwanaki kadan ya rage manoman nan su girbe amfanin gonarsu.

“Kungiyar RIFAN na kira ga Gwamnatin Tarayya ta kawo musu dauki kamar yadda ta yi wa ’yan uwansu a Jihar Kebbi”, inji shi.

Yayin da yake jawabi a madadin manoman da abin ya shafa, Malam Abdulmumini Saya-Saya, ya dora alhakin ambaliyar da ta ja asarar a kan Hukumar  Kula da Kogin Hadeja da Jama’are bisa sakin ruwan madatsun da ta yi zuwa koguna ba tare da sanarwa ba.

Ya yi zargin cewa babu wanda ya ce komai a kan wannan lamari da ya janyo amfanin gonakin manoma ya bi ruwa.