✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Malamin sakandiren Najeriya ya kusa lashe gasar Dala Miliyan 1

Dan Najeriya na cikin mutum goma da suka rage a gasar Global Teacher Prize 2020.

Malamin makarantar sakandaren jeka-ka-dawo (GDSS) ta Karu, a Abuja, Olasunkanmi Opeifa, na gab da lashe gasar malaman makaranta ta duniya, wadda zai samu kyautar dalar Amurka miliyan daya.

A yanzu haka malamin ya yi nasarar shiga cikin goman farko na malaman da suka rage, cikin mutum 12,000 da suka shiga gasar daga kasashe 140 na duniya.

Kungiyar Varkey Foundation, tare da hadin gwiwar sashen Ilimi da Kimiyya da kuma Al’adu na Majalisar Dinkin Duniya, ya shirya gasar mai taken: “Global Teacher Prize 2020″.

Stephen Fry, daya daga cikin alkalan gasar, kuma sanannen mai wasan barkwanci na Turanci, ya bayyana nasarar da Opeifa ya yi a sakon bidiyo da fitar.

“Yau, ina farin cikin na sanar da cewa, Olasunkanmi Opeifa, dan Najeriya na cikin mutum goma da suka rage a gasar Global Teacher Prize 2020.

“Olasunkanmi, ka sanya wa daliban ka sha’awar koyon yaren Ingilishi ta hanyar barkwanci (edutainment- fun-based learning) da saukin koyan rubutu ta hanyar rawa da koyar da fitar da sauti ta hanyar waken sauri da hikimomin karya harshe.

“Ka kuma wallafa littafi kan koyon Ingilishi domin ka fadada koyarwarka fiye da garinku, ka kuma sadaukar da hutun ka na karshen mako domin tabbatar da dalibanka sun kammala manhajar karatunsu.

“Da irin salon koyarwar nan, sakamakon jarrabawar makarantar ya kara kyau sosai, har da yawa daga cikin dalibanka suka samu sakamakon shiga jami’a.

Ina taya ka murna Olasunkanmi da jinjina maka kan duk abubuwan da ka yi.”

Haka kuma Mataimakin Babban Darektan ilimi na UNESCO, Stefania Giannini, ya ce “Muna taya Olasunkanmi Opeifa murnar zabarsa da aka yi cikin zakaru 10, daga cikin dimbin malamai masu hikima da jajircewa.

“Ina fatan labarin nan zai kara wa masu niyyar shiga layin koyarwa kwarin gwiwa, ya kuma fito da fasahar da malamai ke amfani da ita a Najeriya da duniya baki daya.” inji Giannini.

Sauran abokan takarar Olasunkanmi sun hada da: Malamai daga kasar Ingila, Jamie Frost, da Malamin kasar Italiya Carlo Mazzone; da Malaman kasar Afirka ta Kudu, Mokhudu Cynthia Machaba, da Malama ‘yar kasar Amurka, Leah Juelke da kuma Malamar kasar Koriya ta Kudu, Yun Jeong-hyun.

Sauran hudun za a bayyana sunayen su daya bayan daya a kowane mako.