✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malami ya shiga hannun DSS kan yi wa dalibarsa fyade

Ana gudanar da bincike kan lamarin.

Jami’an tsaron DSS sun kama wani malami a Jihar Osun bisa zargin yi wa wata dalibarsa ’yar aji biyu a karamar sakandare ’yar shekara 16 fyade har ta dauki ciki.

An kuma zargi wata malamar makarantar da yunkurin zubar da cikin.

Wata mai fafutukar kare hakkin dan Adam, Citizen Lola Wey, ce ta kai rahoto faruwar lamarin ga hukumar DSS domin a bi wa yarinyar hakkinta.

Dalibar ta bayyana cewa, “Malaminmu ya ce na je gidansa na karbi littafina na koyon Faransanci.

“Da na isa sai ya kai ni dakinsa, daga baya na gane cewa shi kadai ne a gidan.

“Na yi ihu don neman taimako amma babu wanda ya zo. Haka ya cire min kayana ya yi min fyade.”

Ana ci gaba da tsare malamin domin gudanar da cikakken bincike kan lamarin.