✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malami ya sace dalibinsa ya kashe bayan ya karbi kudin fansa

Ana zargin wani matashi da sace dan makwabcinsa wanda kuma yake karantar da shi bayan ya yi garkuwa da shi, ya karbi kudin fansa inda…

Ana zargin wani matashi da sace dan makwabcinsa wanda kuma yake karantar da shi bayan ya yi garkuwa da shi, ya karbi kudin fansa inda a karshe ya kashe shi. Lamarin wanda ya faru a kauyen Hayin Gada Zabi da ke Karamar Hukumar Sabon Gari a Jihar Kaduna ya jefa mutanen kauyen a cikin tashin hankali bayan da asirin wanda ake zargin ya tonu.

Wanda ake zargi mai suna Ahmadu Abdullahi Yahaya mai shekara 20, ya sace dan makwabcinsa mai suna Muhammadu Bello Shehu mai shekara 14 wanda dukansu suna zaune ne a kauyen ne kuma gida daya ne a tsakanin gidajensu.

Aminiya ta tattauna da mahafin marigayin mai suna Shehu Abubakar, wanda ya ce kwana 22 da suka gabata ya tura dansa Bello kiwon tumaki kuma da misalin karfe 5:00 na yamma da zai kai yayansa Marabar Gwanda don a yi masa allura ya wuce shi yana kiwon tumakin, “Bayan na dawo ne sai na ga tumakin na yawo su kadai babu Bello tare da su sai na tsaya ina nemansa ban gan shi ba har na shiga cikin gonaki ina ta kira ina nemansa amma shiru, sai na koro tumakin zuwa gida na tambaya aka ce bai dawo ba. Tsammanina ko ya yi wa wani barna ne a gona, sai muka bazama nema har dare ya yi Allah bai sa mun gan shi ba, sai muka hakura muka dawo gida. Washegari muka ci gaba da nema can sai aka kira wayata aka ce danka na hannunmu amma sai ka kawo Naira miliyan biyar. Sai aka kashe wayar, ba a sake kira ba sai washegari misalin karfe 12:00 na rana sai aka kara kira, suka kara cewa a kawo Naira miliyan biyar,” inji mahaifin.

Ya kara da cewa: “Sai na ce musu ina na ga Naira miliyan biyar. Sai suka ce ai kana da kudi, na ce ba ni da kudi amma ina da kadara, sai suka ce in kawo Naira miliyan biyu. Kai in takaita maka haka muka yi ta yi a karshe dai muka tsaya a kan Naira dubu 60. Sai na ce to ina zan kai muku kuma a ina zan samu dana? Sai suka ce za su kira ni su gaya min. To misalin karfe 7:00 na yamma sai suka kira ni da wannan lambar da suke kirana cewa in kawo musu a kan hanyar Zabi, to ni da kanen matata muka tafi kai musu kudin muna tafiya sai su rika cewa ka zo muna ganinku ka kara biyo hanya za mu hadu har dai ni na tsaya a wani wuri na ce shi kanen matar tawa ya karasa ya kai musu ina hangensa ya kai musu inda suka ce a kai musu kudin a ajiye.”

Game da ko ya sanar da jami’in tsaro ko wata hukuma sai ya ce, “Mun yi shawara zuwa mu fada wa hukuma sai na ce a’a a saurara tunda sun nemi a ba su kudi, kuma an shirya za a a ba su to kawai mu ba su mu huta domin kada su gane cewa an fada wa hukuma su kashe yaro tunda suna lura da duk abin da ake yi dalilin da ya sa ba mu fada wa hukuma ba, amma mai unguwa ya sani tunda muna tare da shi.”

Malam Shehu ya ce bayan kai kudi da kimanin kwana 15 yaro bai dawo ba “Sai muka dunguma zuwa wajen Dagacinmu muka sanar da shi cewa har yanzu ba a dawo da yaro ba bayan sun nemi Naira dubu 60 kuma mun kai musu, sai Dagaci ya ce to zai turo ’yan sanda domin a yi bincike. Bayan Dagacin ya turo ’yan sanda ne suka kama mutum uku wadanda ake zargi da sa hannunsu, aka kama har da kanen matata Kabiru wanda ya kai kudin da wani mai suna Ali da Sa’idu, bayan an kama su na’yan kwanaki, an yi musu tambayoyi sai aka sako su, to sai aka bibiyi lambar da ake kirana da ita sai ga wani sako da aka tura wa wani Malam Bilya kuma shi abokin wanda aka kama ya zo ta hanyar tantance layin wayar da ake kirana da ita kuma shi wanda aka kama ake zargi mai suna Ahmadu makwabcinmu ne, kuma  shi ne ya je ya nuna mana inda gawar yaron nawa take a wani daji. Wallahi gawar yaron cikin wani yanayi an raba kai da gangar jiki, kuma hannaye daban sai dai da wando ajikin gawar Bello ga kuma takalmansa a waje daya haka aka kwashe sauran abin da aka tarar na ragowar jikin gawar Bello, mu da ’yan sanda muka kai Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika aka aje daga baya ’yan sanda suka ba mu gawar bayan likitoci sun kammala bincikensu, a yau Juma’a (12/10/2018) muka yi mata sutura.

Wata majiya ta ce wanda ake zargi kwanan nan aka karbo shi daga gida yari bayan kwashe wata biyu yana tsare bisa tuhumarsa da yunkurin kashe kanensa. Mahaifin wanda ake zargin Malam Abdullahi Yahaya Ahmed ya ce ba zargi ba ne an kama shi ne da hannu dumu-dumu a kan sace dan makwabta da kashe shi bayan ya karbi kudi a hannun uban yaron.

Malam Abdullahi ya ce, “Kwanan nan na karbo shi daga gidan yari tare da taimakon su makwabtan nawa a kan yunkurin kashe dan uwansa da ya dawo daga neman kudi, kuma har yanzu maganar ba ta kare ba sai kuma ga wannan. Don haka ni na sallama shi domin ni ban san ina ya koyi irin wannan muguwar dabi’a ba, da bakinsa yake ba da labarin yadda ya yi har ya sace yaron kuma ya kashe shi, kuma ya ce shi kadai ya yi babu wanda ya sa masa hannu, kuma yana daga cikin malaman da ke koyar da yaron, ka ga wannan ai cin amana ne.”

Kakakin ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu A. Sabo wanda ya tabbatar da faruwan lamarin, ya ce sun kama Ahmad Abdullahi kuma ya fara ba su hadin kai a binciken da suke yi, kuma bayan sun kammala za su kira manema labarai su bayyana musu duk abin da ake ciki.