✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malam Shekarau ina gaskiyar lamari?

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Malam Ibrahim shekarau kan lallai ya fito ya bayyana wa jama’a gaskiyar lamarin shirinsa na…

Editan Aminiya ka ba ni dama in yi kira ga Malam Ibrahim shekarau kan lallai ya fito ya bayyana wa jama’a gaskiyar lamarin shirinsa na komawa jam’iyyar PDP. Ko Malam yana da masaniyar ’yan Najeriya sun gaji da mulkin PDP, kuma wane irin gyara yake son kawowa? Tunda Gwamna Kwankwaso ya koma, ai karin karfi ne ga jam’iyyar APC, amma ja-in-jar da Malam ke yi masa na iya kawo tarnaki a jam’iyyar. Mu dai talakawa muna addu’ar Allah Ya sa manyanmu su gane, su bi tafarki madaidaici don tabbatar da adalci ga al’umma a siyasar Najeriya. Da fatan Malam ya dauki nasihata. Idan Kwankwaso Allah Ya bai wa girma, sai a bisu; idan suka karkace a ba su shawara, wannan ita ce masalaha, ba adawa mara tushe ba. Daga Ahmad Tiga 08068643445.

Sakonnin waya

Ga Guddurawa da Katagumawa
Assalamu alaikum ina mai mika sakona ga mutanen Guddurawa da Katagumawa da su hada kansu, kada su bari a sake wulakantamu a zabe mai zuwa na 2015, in Allah Ya kaimu. Daga Jamilu dahiru Sakuwa. 07063324603.

Aisha ta yi hangen nesa
Editan Aminiya, na yaba da tunani da hangen nesa, da kuma nuna kishin kasa da wata  Malama Aisha Usman Liman ta nuna cikin takardar da ta rubuto tana ba ‘uwanmu ’yan kungiyar Ahlus sunna lil da’awati hakuri. Don Allah su duba su kuma lura da abin da wannan takardar ta kunsa, a kuma yi aiki da ita, don samun sauki ga Muslmi da Arewa. Daga Zauro Abdullahi 08069077363.

Ga Kiristocin Jihar Katsina
Edita don Allah ka ba ni damar yin kira ga kiristocin Jihar Katsina mai albarka, kan su yi amfani da bikin murnar haihuwar Yesu Almasihu, wajen addu’ar ci gaba da daukaka ga Gwamna Shema da jihar Katsina da kasa baki daya, tare da addu’ar zaman lafiya. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.

Ga ’yan Arewa
Ana zargin wasu manyan ’yan arewa da karbar toshiyar baki, don su goya wa Shugaba Jonathan baya. Daga Abubakar Altine Yabo 08037620311.

Gaisuwa ga Gwamnan Katsina
Assalamu alaikum, Aminiya don Allah ku mika min gaisuwata ga Gwamnan Katsina. Bayan haka ku fada masa wallahi kudin tallafin karatu (Scholarship) da ya ba mu, to ba kowa ne yake samu ba. Daga Anas Honesty, Tudun Wada Funtua. 08034004515.

Taya murna ga kiristocin Jihar Katsina
Ina taya mabiya addinin Kirista murnar bukukuwan Kirsimeti. Daga Mu’azu Safiyanu danja, Jihar Katsina 08054639924.

Ga Gwamna Shema
Mu dai ’yan Karaduwa ba mu amfana da komai daga Gwamnatin Shema, sai farfagandar ba mu da ’yan siyasa, masu kishin al’umma; sai masu kishin aljihunsu; ba mu da uwa a gindin murhu. Don haka duk wani muhimmin abu sai mu ji labari. Jami’a da Kwalejin Kimiyya da Fasaha babu wadda aka ba mu. Gwamna Shema ka rika yi mana adalci. Daga Jamil Medicine Malumfashi 08021214785.

Ga Shugaban Hukumar Zaben Kano
Edita ina so ka isar mini da sakon fatan alheri ga shugaban hukumar zabe ta Jihar Kano, Dokta Sani Lawan Malumfashi, a bisa kokarin jan hankali da wayar da kan al’umma da yake yi. Daga Khamis Imam Bashir Gama C 08030932677.

Edita na shakulatun bangaroda Amini
Assalamu alaikum. Haba Aminiya kada a ganmu a rana ke da mininki. Domin nga Edita ka dauko hanyar haka. Na gaji da rubuto sako, a kalla sau uku a mako. Edita na g akana shakulatun bangaro da amini. Daga danlitti Pillars Rimin Kebe Kano 07037874889.

Gaisuwa ga Malam Shekarau
 Salam. Aminiya ina so ku mika min gaisuwa ga Mai girma Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, tare da daukacin ’yan uwa masoya Ananbi (SAW). Daga Mariya Musa Fagge. 08113767397.

Ga ’yan Buhariyya da Shekariyya
Kirana ga wasu bangarori na Buhariyya da Shekariyya, da cewa su dinke barakar d ake tsakaninsu; ko kuma mu daina APC. Daga Sulaiman SBK. 07038999155.

APC muna tare
Aminiya ku tiamaka ku b ani fili in mika sakona ga jam’iyyar APC a kan muna tare das u dari bisa dari. Kuma su kara hada kansu, ba wariya. Allah Ya kaimu shekarar 2015. Daga Alhaji Kankat. 07061316464.

Ga Gwamnan Bauchi
Assalamu alaikum. Don Allah Aminiya ku mika min sako ga Gwamnan Jihar Bauchi, Malam Isa Yuguda kan sababbin hakimai da ya nada. Wannan nadi ya kawo mana rashin zaman lafiya a garin Bidir, da fatan za a duba mu, don mu samu kwanciyar hankali da zaman lafiya. Daga Murtala Idris Katagum Azare 08181137443.

Ga masu dokin APC
Salam Edita, sakona ga mutanen da ke ta dokin APC, ton in dai APC ta ci zafe, kamar yadda mutanen Legas cikin kashi uku, kasha biyu suka yi gudun hijira da baki da ’yan gari, idan Buhari ya ci Allah kadai yasan yawan wadanda za su yi hijira. Fatanmu shekara ta 2015 ta samu gwanin direba . Daga Yakubu Fulatan Jihar Kano 08068805058, 07032854122, 08076714604.

Tambaya ga Edita
Ina tambayar Editan Aminiya, me yasa aka daina kawo mana shafin ‘Dausayin kauna’?. Daga Nazifi Kano 070387752013.

Hukumar zabe ke murdiya
’Yan uwa ’yan Najeriya, mu daina ganin laifin PDP a magudin zabe, don Hukumar Zabe ta INECe ke karbar kudi, su mured mana zabe. Shugabannin INEC ku sani ba a zuwa kiyama da kudi, sai abinda mutum ya aikata; mai kyau, ko mara kyau. Daga Isah Dilwaha Abuja.  08059044449.

Jinjina ga PDP tsantsa
Salam Edita, ka ba ni dama in yi jinjina ga PDP tsantsa, da tsohon minista, mataimakin Gwamna Mukhtar Shagari. Allah Ya taimakeka a 2015, ka zamo gwamnan Sakkwato. Daga Bello Dandin Mahe Suleja 08098102922