✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Malam Iro fi Jahannama

Wani Bakane ne mai suna Malam Iro ya je aikin Hajji, bayan sun isa an kai su masauki sun huta kowa ya aje kayansa, sai…

Wani Bakane ne mai suna Malam Iro ya je aikin Hajji, bayan sun isa an kai su masauki sun huta kowa ya aje kayansa, sai ’yan uwansa suka fita aka bar shi shi kadai a daki. Can Allah Ya kawo gobara a dakin, ya rasa yadda zai yi, ya fito waje da gudu ya ga duk Larabawa ne kuma ba ya jin Larabci ya ga ba dama, sai ya mike a guje yana cewa ‘’Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun! Malam Iro fin nar!” Ya ga ba a kula shi ba. Sai ya ce da karfi ‘’Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un. Malam Iro fi Jahannama!”
Umar Musa Gwadabawa, Tudun Wada, Sakkwato. 07065747515