✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Makarantar Koyon Sana’a ta Kazaure na cikin mawuyacin hali’

Malam Yahaya Kazaure mai makarantar koya wa matasa da ’yan mata sana’o’i a kauyen Karaftayi da ke garin Kazaure a Jihar Jigawa, ya koka game…

Malam Yahaya Kazaure mai makarantar koya wa matasa da ’yan mata sana’o’i a kauyen Karaftayi da ke garin Kazaure a Jihar Jigawa, ya koka game da karancin kayan koya wa matasa sana’ar da za su dogara da kansu.
Ya ce ya shafe shekara fiye da goma yana koya wa matasa da yara dinkin keke da saka da rini da yin aikin gadaje, ta hanyar amfani da kayan aro wadda wani lokacin ma saboda karancin kayan aikin baya iya koya wa dalibansa abin da ya kamata su koya, sai dai a yi musu a rubuce a kan allo.
Ya yaba wa wata mata da ta dubi halin da makarantar take ciki ta ba shi kyautar kekunan dinki uku da injin saka domin ci gaba da koya wa dalibansa.
“Hakan ya dan inganta al’amura, inda aka samu karuwar dalibai a makarantar, inda kafin ta bada tallafin dalibai suka daina zuwa makarantar.” Inji shi.
Ya ce dole ne ya gode wa masarautar Kazaure saboda kokarin da take wajen taimaka wa makarantar.
Ya ce “Masarautar Kazaure ta ba ni tallafi daban-daban, wanda hakan ya sa har yanzu makarantar ba ta durkushe ba. Ina fata hukumar NDE reshen Jihar Jigawa za ta cika mini alkawarin da ta dauka na cewa za ta tallafa mana, inda har yanzu ba mu ga komai ba. Sannan ina kira ga iyayen yara da masu kudi da su taimaka wa makarantar don ta ci gaba da tsayawa da kafafunta, musamman ma tun da tsawon shekarun da na shafe ina koya wa yara da matasa ban taba karbar ko da Naira daya daga wurinsu ba, ina yin komai don Allah ne.”
Ya ce daliban da ke koyon sana’o’i a makarantarsa sun kai 2,000, inda masu zuwa da yamma koyon dinki yawansu ya kai 500; masu sakar zamani 700, masu koyon kitso mutum 200 da masu yaki da jahilci mutum 300
Ya ce yana amfani da kudin da yake samu daga aski da dinki wajen ba masu yi wa hidima kasa da suke taimaka masa alawus dinsu a karshen wata.
“Don haka ina rokon karamar Hukumar Roni da Kazaure da su dauki nauyin masu yi wa kasa hidimar da suke taimaka mini.”
Ya bukaci gwamnatin Jihar Jigawa ta taimaka wa makarantar don a samu matasa da yara da za su iya dogara da kansu ba wai a kan gwamnati ba.