Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya bukaci Gwamnatin Tarayya ta tura sojoji don samar da tsaro a makarantu a kowane lokaci.
Da yake yin tir da garkuwa da aka yi da dalibai da ma’aikata a Kwalejin Kimiyya ta Gwamnatin Tarayya da ke garin Kagara a Jihar Neja, Atiku ya bukaci Gwamnatin da ta a ayyana makarantun firamare da na sakandare a matsayin wurare masu cikakken tsaro.
- An zargi miji da dukan matarsa har sai da ta ce ga garinku nan
- Matashi ya kashe kansa ta hanyar yanke gabansa a Kano
- Sojoji 6 sun rasu bayan Boko Haram ta tarwatsa su ta kwashi makamai
“Idan girke sojoji dauke da makamai ba za ta yiwu ba a makarantu, sai kowace jiha ta kafa jami’an tsaron sa-kai — yadda Jihar Borno ta yi kuma ta ga amfanin hakan — a tura su makarantu tare da jami’an ‘Civil Defence’.
“Kar mu nade hannuwa mu ki yin komai; muna da uzuri idan muka dauki mataki ko da daga baya za mu gane cewa kuskure ne fiye da idan muka zura ido muka ki yin komai.
“A matsayinmu na kasa wajibi ne mu samar da cikakken tsaro ga makarantun ’ya’yan talakawa kwatankwacin na makarantun ’ya’yan manya,” inji Atiku.
Ya ci gaba da cewa, “Matsalar tsaro a Najeriya ta kai intaha, musamman ganin yadda take ritsawa da kananan yara.
“Abin da ya kamata shi ne a nemi mafita ba neman wanda za a dora wa laifi ba.
“Yanzu dai mun fahimci cewa biyan kudin fansa da barin masu laifi suna cin ribar manyan laifukan da suka aikata ba ita ba ce mafita.
“Idan kuma kasance muna biyan masu aikata manyan laifuka, abin da zai biyo baya shi ne karuwarsu.
“Babban abin da zai kawo karshen wannan babbar matsala a Najeriya shi ne a tabbatar da hukunta masu laifi yadda ya kamata.
“Wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da aiwatar da hukuncin da dokar kasa ta tanada ga masu satar mutane ta hanyar kame su da gurfanar da su a gaban kotu saboda wadanda aka kama da laifi za su zama izina ga wasu.”