Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci da Rashawa (PCACC), Barista Muhyi Magaji Rimin Gado saboda kin karbar sabon akantan da Akanta Janar na Jihar Kano ya tura wa hukumar.
Dakatarwar, wacce ta fara aiki nan take, ta biyo bayan samun takardar korafi da Majalisar ta yi daga Ofishin Akanta Janar din ne a kan lamarin.
“Bayan kin karbar akantan, har ma takardar kora aka rubuta mishi”, inji wata sanarwa da Jami’in Hulda da ’Yan Jarida na Majalisar, Uba Abdullahi, ya fitar.
Takardar Akanta Janar din dai ta ce Shugaban na PCACC ya nada wani ma’aikaci da ke mataki na hudu a matsayin akantan Hukumar, lamarin da ta ce ya saba da dokokin aikin gwamnati a Jihar.
Bayan doguwar muhawara a tsakanin ’yan majalisa, gidan ya amince da matakin dakatar da Barista Muhuyi har tsawon wata daya.
Rahoton Kwamiti
Shugaban Masu Rinjaye Alhaji Labaran Abdul Madari ya nemi Majalisar da ta danka lamarin ga kwamitinta mai kula da yaki da cin hanci da rashawa don fadada bincike tare da daukar mataki.
Kwamitin dai na karkashin jagorancin Honorabil Umar Musa Gama ne.
Sauran mambobin Kwamitin sun hada da Shugaban Kwamitin Shari’a Honorabil Lawan Shehu da Honorabil Salisu Ibrahim Doguwa da Honorabil Magaji Dahiru Zarewa da Honorabil Sale Ahmad Marke.
Har ila yau Majalisar ta ba Kwamitin wa’adin makonni biyu da ya mika mata rahoton bincikensa.
Da yake yi wa manema labarai karin haske, Sugaban Masu Rinjaye na Majalisar ya bayyana cewa Akanta Janar yana da damar tura akantoci dukkanin ma’aikatun gwamnati.
“Akwai dokar jihar Kano a sashe na 28d ta ce ta ba Akanta Janar damar tura akantoci dukkanin hukumomin gwamnati.
“A gefe guda kuma shi ma ma’aikacin ya rubuta wa Akanta Janar din korafi a kan kin karbarsa da aka yi.
“Hakan ya sa ya rubuto wa Majalisa korafi domin ta bi kadin lamarin”, inji Honorabil Madari.
Damar bincike
Shugaban Masu Rinjayen ya kara da cewa Majalisar ta dakatar da shugaban hukumar ta PCACC ne domin samun cikakkiyar damar yin bincike a kan lamarin.
A makon jiya ne dai wasu rahotanni suka nuna cewa gwamnatin jihar ta Kano tana matsa wa majalisar lamba a kan ta sauke Barista Muhuyi saboda binciken da ya kaddamar a kan wasu dangin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwatito cewa yayin da Majalisar ke shirin fara gudanar da bincike a kan PCACC din, gwamnatin jihar ta ma riga tura wani jami’i daga Ofishin Akanta-Janar don ya maye gurbin akantan hukumar.