Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bayar da umarnin dakatar da dukkan gine-ginen shaguna a harabar Masallacin Juma’a na Fagge da ke birnin Kano.
Matakin na zuwa ne kwana daya bayan fitaccen malamin addinin Musuluncin nan na Kano, Sheik Tijjani Bala Kalarawi ya sanar da ajiye mukaminsa a matsayin mamba na kwamitin masallacin.
- NAFDAC ta gargadi ’yan Najeriya kan cin kajin da aka yi fasa-kwaurinsu
- A shirye Najeriya take ta taimaka wa Sudan ta Kudu — Buhari
Malamin dai na zargin an kacaccala masallaci, wanda shi ne masallaci Juma’a mafi fadi a kwaryar birnin Kano, wajen gina shaguna ba tare an san inda kudin hayarsu suke tafiya ba, ko kuma yin amfani da su wajen kula da shi.
Majalisar, a yayin zamanta na ranar Talata, karkashin Shugabanta, Hamisu Ibrahim Chidari ta umarci a dakatar da dukkan gine-ginen shaguna, sannan ta kafa kwamitin mutum tara don ya bincika zarge-zargen da ake yi.
Hakan dai ya biyo bayan wani kudurin gaggawa da mamba mai wakiltar mazabar Dala a majalisar, Lawal Hussaini ya gabatar a kan batun.
Dan majalisar ya bayyana abin da ke faruwa a msallacin a matsayin abin takiaci, tare da bukatar majalisar ta gaggauta dakatar da hakan don amfanin al’umma.
Bayan tafka muhawara, majalisar ta amince da kafa wani kwamitin mutum tara, wanda zai kasance karkashin jagorancin Muhammad Uba Gurijya, dan majalisa mai wakiltar mazabar Bunkure.
Sauran mabobin kwamitin sun hada da Sunusi Usman Bataiya da Magaji Dahiru Zarewa da Nuhu Abdullahi Achika da Lawan Hussaini da Abubakar Dalladi Isa Kademi da Muhammad Tukur da Sale Ahmed Marke, yayin da Mataimakin Daraktan Shari’a na majalisar zai kasance Sakataren kwamitin.
A ’yan kwanakin nan dai, an sha zargin sayar da wuraren gwamnati da dama a Jihar Kano, yayin da wasu kuma ake amfani da su wajen giggina shagunan kasuwanci.