✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisar Jihar Gombe ta tsige Mataimakin Shugaban Majalisar

Majalisar dokokin jihar Gombe yau Talata ta tsige mataimakin shugaban Majalisar Honorabul Shu’aibu Adamu Haruna, wanda yake wakiltar mazabar Kwami ta Gabas a jihar. ‘Yan…

Majalisar dokokin jihar Gombe yau Talata ta tsige mataimakin shugaban Majalisar Honorabul Shu’aibu Adamu Haruna, wanda yake wakiltar mazabar Kwami ta Gabas a jihar. ‘Yan majalisar sun maye gurbinsa da Honorabul Siddi Buba daga mazabar Kwami ta Yamma a matsayin sabon Mataimakin Shugaban Majalisar.

Dan Majalisa Honorabul Adamu Saleh Pata, daga mazabar Yamaltu ta Gabas ne ya gabatar da kudirin tsige Mataimakin Shugaban Majalisar Honorabul Shu’aibu Adamu Haruna. Yayin da Dan Majalisa daga mazabar Billiri, Tulfugut Meme Kardi, ya amince da tsige mataimakin shugaban Majalisar.

‘Yan Majalisa 21 ne suka rattaba hannun tsige mataimakin shugaban Majalisar Honorabul Shu’aibu Adamu Haruna.