Majalisar Dokokin Jihar Gombe ta jajanta wa Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Tasi’u Maigari, bisa iftila’in gobarar da ta cinye wani bangare na zauren majalisar.
Sakon da Babban Jami’in Yada Labarai na Majalisar, Abubakar Muhammad Umar, ya fitar, ta bayyana girgizar Majalisar da samun labarin gobarar, a daidai lokacin da al’ummar Katsina suke farfadowa daga gobarar Babbar Kasuwar Katsina.
- Harin Geidam: Sojoji sun kashe ’yan Boko Haram 21
- ’Yan siyasa sun fara lika fosta a jikin dabbobi
- Sojoji sun kama makamai a fadar sarakunan Binuwai
Sakon ya ce Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Gombe, Abubakar Muhammad Luggerewo, ya ce Katsinawa mutane ne masu tawakkali, don haka su dauki gobarar a matsayin kaddara, su kuma roki Allah Ya ba su hakurin jure iftila’in.
Daga karshe ya tabbatar wa da Majalisar ta Katsina da cewa za su ci gaba da taya su addu’ar Allah Ya kare sake aukuwar hakan, Ya Kuma mayar musu da mafi alherin asarar da suka yi.