Majalisar Dokokin Kano ta amince da kwamishinoni 17 daga cikin 19 da gwamnan jihar, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya aike mata.
Majalisar dai ta amince da mataimakin gwamnan Kwamred Aminu Abdussalam ba tare da tantancewa ba.
Sannan ta amince da mutane 16 bayan da ta tantance su.
Gwamnan Kano ya tura wa Majalisa sunayen kwamishinoni 19
Gwamnan Kogi ya kori Kwamishina da wasu 2 daga aiki
Mutanen sun haɗa da, shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Umar Haruna Doguwa, tshohon shugaban ma’aikatan fadar gwamnatin jihar Kano, Ali Haruna Makoda, tsohon kwamishinan lafiya Dr. Abubakar Labaran Yusuf, da tsohon shugaban riƙo na ƙaramar hukumar Gwale Abbas Sani Abbas.
Sauran sun haɗa da Ɗanjuma Mahmud, Musa Sulaiman Shanono, Ladidi Garko, Marwan Ahmad, Muhd Diggol, Adamu Aliyu Kibiya, Dr. Yusuf Ibrahim Kofar Mata, Safiyanu Hamza, Tajuddeen Othman Ungogo, Nasiru Sule Garo, Barista Haruna Isa Dederi da kuma Baba Halilu Dantiye.
Amma akwai ragowar biyu da Majalisar ba ta tantance ba saboda sun tafi aikin Hajji.
Waɗannan su ne Sheikh Tijjani Auwal da kuma Hajiya Aisha Lawan Saji.