Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya yi wa sabon Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Nuhu Bamalli murnar nadin da aka yi masa.
Ahmed Lawan ya bayyana nadin Alhaji Bamalli a matsayin wanda ya dace, duba da kwarewarsa da kuma kyawawan dabi’u.
- Bayan shekara 100 Sarautar Zazzau ta koma gidan Mallawa
- Sarkin Zazzau: Masu Zaben Sarki sun yi mubaya’a
Shugaban Majalisar ya yi fatar sarkin zai yi dukkan mai yiwuwa wajn biyan bukatun jama’ar Masarautar Zazzau da aka ba shi amanar su.
Ya kuma taya jama’ar Zazzau da Gwamnatin Jihar Kaduna murna bisa yadda aka nada sabon sarkin ba tare da tashin hankali ba.
Sarki Ahmed Nuhu Bamalli ya fara jagorantar Masarautar Zazzau ne ranar Laraba, 7 ga Oktoba, 2020 a matsayin Sarki na 19.
Shi ne na da aka samu daga gidan Mallawa bayan shekara 100, tun bayan sarautar kakansa, Sarki na 13, Alu Dan Sidi a 1920.
Sarki na 18, Alhaji Shehu Idris, ya rasu bayan jagorantar masarautar na tsawon shekara 45, yana da shekaru 84.
Tuni dai Masu Zabar Sarki na Masarautar suka yi mubaya’a ga Sarki Ahmed, wanda Yariman Zazzau, Alhaji Munir Ja’afaru ya ce nadinsa nufin Allah ne.
Munir Ja’afaru wanda shi ma ya nemi hawa kujerar, a sakonsa na taya murna ya jaddada muhimmnacin mara wa Sarkin Zazzau na 19 baya.
Ya roki Allah Ya yi masa jagora, Ya kuma tabbatar da zaman lafiya a masarautar.