✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta sauke Shugaban karamar Hukumar Jahun

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta sauke Shugaban karamar Hukumar Jahun Alhaji Musa Harbo tare da dakatar da takwaransa na karamar Hukumar Gumel Alhaji Ala Gumel…

Majalisar Dokokin Jihar Jigawa ta sauke Shugaban karamar Hukumar Jahun Alhaji Musa Harbo tare da dakatar da takwaransa na karamar Hukumar Gumel Alhaji Ala Gumel da na karamar Hukumar Birniwa Malam Alhasan Babandi, sakamakon samunsu da almundahana bayan da ta kafa kwamatin bincike a kansu a kwanakin baya.
Majalisar ta kafa kwamatin ne domin ya bincika wa gwamnatin jihar yadda shugabanniñ kananan hukumomin jihar 27 suke kashe dukiyar jama’a musamman kudin da suke amsa daga Asusun Tarayya da ke zuwa ta hannun jihohi.
A ranar 24 ga Yunin da ya gabata ne majalisar ta kafa kwamatin, inda a cikin rahotonsa ya shawarce ta da ta sauke Shugaban karamar Hukumar Jahun daga mukaminsa saboda an same shi da almubazaranci da kudin jama’a tare da rashin zuwa ofis, lamarin da ya saba wa sashi na 9 na dokokin kananan hukumomi na Jihar Jigawa ta shekarar 2012.
Kwamatin ya kuma bukaci a dakatar da shugabannin kananan hukumomin Birniwa da Gumel saboda samunsu da laifin badakala da yi wa aiki rikon sakainar kashi, har sai kwamatin ya kammala bincikensa.
Mataimakin Shugaban Majalisar Alhaji Muhammed Garba ne ya jagoranci zaman majalisar a ranar Alhamis din makon jiya inda suka yanke wannan hukunci bayan karbar rahoton kwamitin.