Majalisar Dattijai ta amince da bukatar Shugaba Muhammadu Buhari ta ciyo bashin Naira tiriliyan 2.3 (kwatankwacin Dala biliyan 6.183) don cike gibin kasafin kudin 2021.
Wannan na zuwa ne bayan la’akari da rahoton da kwamitin da ke sa ido a kan basussukan cikin gida da na waje a karkashin jagorancin Sanata Clifford Ordia (PDP, Edo) ya gabatar, .
“Mun kiyasta cewa Najeriya za ta iya tara Dala biliyan 3 ko sama da haka, amma ba zai wuce Dala biliyan 6.183 (adadin da aka bayar a cikin dokar kasafin kudin 2021) ba a cikin hadakar bashin shekara biyar zuwa 30,” a cewar Buhari.
A watan Mayu, Shugaba Buhari ya nemi amincewar Majalisar Dokokin Najeriya don nemo hanyoyin samun kudi ciki har da cibiyoyin kudi na duniya.
Ya bayyana cewa rancen zai bai wa Gwamnatin Tarayya damar gudanar da muhimman ayyukan more rayuwa a bangaren sufuri, da kiwon lafiya, da ilimi da sauransu.
Kazalika, Majalisar Dattawan ta amince da bukatar Shugaba Buhari ta sayar da takardun lamuni na Eurobond wadanda suka kai Dala biliyan 3 amma ba su wuce Dala biliyan 6.1 ba a Kasuwar Hadahadar Kudade ta Duniya, don samar da rancen da ake bukata don cike gibin kasafin kudin na 2021.
Majalisar ta kuma amince da shawarar da kwamitin ya bayar cewa a nemo kudin ta hanyoyi daban-daban ciki har da Kasuwar Hadahadar Kudi ta Duniya da wasu hanyoyin na daban.
Ta kuma umarci Ministar Kudi da Kasafi da Tsare-tsare, da Darakta-Janar na Ofishin Kula da Basussukan da ake Bin Gwamnati, da Gwamnan Babban Bankin Najeriya, su mika wa Majalisar Dokoki, a cikin kwanaki 10, takarda dauke da adadin Dalar Amurka da aka samu ta hanyar amfani da hanyoyin da aka amince da su.