✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Majalisa ta amince da Obiora mataimakin shugaban CBN

A yau Alhamis ne Majalisar Dattawa ta tabbatarwa Dakta Kingsley Obiora, mukaminsa da aka ba shi a matsayin mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) bayan…

A yau Alhamis ne Majalisar Dattawa ta tabbatarwa Dakta Kingsley Obiora, mukaminsa da aka ba shi a matsayin mataimakin Gwamnan babban bankin Najeriya (CBN) bayan da shugaba Buhari ya aikawa majalisar kudirin a ranar 12 ga watan Janairun 2020.

Majalisar ta tantance Dakta Kingsley Obiora a ranar Laraba.

Tabbatar masa da mukamin biyo bayan la’akari da rahoton kwamitin majalisar a kan al’amuran a suka shafi bankuna da inshora da sauran bangarorin da suka shafi hada-hadar kudi.

A lokacin da yake gabatar da rahoton ga majalisar Sanata Uba Sani, ya bayyana Dakta Obiora, a matsayin kwararre da ya yi ayyuka a fannin  matakin kasa dama duniya baki daya, ya ce ba a taba tuhumarsa da wani laifi ba dan haka ya dace da mukami wanda ya nemi majalisar ta tabbatar masa.

A lokacin da majalisar ke tantance shi, Dakta Obiyara ya sha alwashin bada gudumawarsa domin ganin babban bankin ya cimma manufofinsa.

Dakta Obiora, zai maye gurbin Dakta Joseph Okwu Nnanna, wanda zai yi ritaya a ranar 2 gawatan Fabarairun 2020.