✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Majalisa ta amince Buhari ya ciyo bashin N7trn daga waje

Majalisa ta ce ayyukan da za a yi da kudaden za su amfani ’yan Najeriya sosai.

Majalisar Dattawa ta amince da bukatar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na ciyo bashin Naira tiriliyan 7.634 daga kasashen waje.

Kudaden da majalisar ta amince a karbo bashinsu a zamanta na ranar Laraba sun hada da Dala biliyan 16.2 da Yuro biliyan daya da kuma Dala miliyan 125, domin aiwatar da muhimman ayyuka a sassan Najeriya.

Majalisar ta amince da bukatar ta shugaban kasar ne bayan sauraron rahoton kwamitinta na basuka, karkashin jagorancin Sanata Clifford Ordia, wanda ya ce, “Kwamitin ya lura cewa wadannan ayyuka, wadanda wasunsu ke bukatar karin kudade za su amfani ’yan Najeriya ta hanyar samar da ayyukan yi, kawar da talauci, bunkasa tattalin arziki, kiwon lafiya, tsaron kasa da kuma samar da ababen more rayuwa.”

Ya ce kwamitin na shawartar zauren Majalisar ya amince “A ci gaba da tattaunwar da ake yi na karbo bashin Dala biliyan 16.230, Yuro biliyan daya da kuma Dala Miliyan 125 karkashin bashin 2018 zuwa 2020 mai dorewa.”

Idan ba a manta ba a watan Satumba, Shugaba Buhari ya aike wa majalisar bukatarsa ta karbo bashin Dala biliyan 4.054 da Yuro miliyna 710 da kuma Dala miliyan 125 domin gudanar da ayyukan raya kasa a Najeriya.

Za a karbo basukan ne daga Bankin Duniya da kuma bankunan kasashen China da Faransa da kuma Bankin Raya Kasashen Afirka da suran cibiyoyin kudi na kasashen duniya.