✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Abin da ya sa na ajiye mukamina —Mailafia

Dalilin tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya na ajiye aiki

Tsohon Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Najeriya (CBN) Obadiah Mailafia ya ajiye mukaminsa saboda kashe-kashen da ake yi a Kudancin Jihar Kaduna, wanda ya ce yana addabar jama’arsa.

Mailafia ya sanar da murabus dinsa a matsayin darakta a Cibiyar Horar da Dabarun Mulki (NIPPS) da ke Kuru, Jihar Filato a ranar Litinin.

“Na yanke shawarar ba zan ci gaba da aiki cikin nutsuwa ba alhali ana ci gaba da yi wa mutane kisan kare dangi.

“Dalilina na ajiye aiki ke nan kuma kwamitin gudanarwar [Cibiyar] ya amshi bukatata; na ba su sanarwar wata daya daga 18 ga Agusta zuwa 19 ga Satumba. Matakin da na dauka shi ne mafi a’ala ga kowa”, kamar yadda ya shaida wa wakilinmu.

Ya bayyana masa haka ne bayan wakilinmu ya nemi jin ko binciken da hukumar tsaro ta DSS ta yi masa a kwanakin baya na da alaka da ajiye aikin da ya yi.

“Na ajiye aiki a NIPPS. Babu wanda ya sa ni ko ya tursasa min. Na yanke shawarar ba zan ci gaba da aiki cikin nutsuwa ba alhali ana ta yi wa mutanena kisan kare dangi.

Gayyata daga ’yan sanda

Wani rahoto na cewa Mailafia ya yi watsi da gayyatar da hedikwatar Rundunar ’Yan Sandan Najeriya ta yi masa, wanda lauyansa Yakubu Bawa ya ce an mika musu ta Ofishin Mataimakin Sufeto Janar na ’Yan Sandan Najeriya a bangaren Binciken Manyan Laifuka.

Barista Bawa ya ce salon gayyatar ya saba tsarin da aka saba gani, yana mai zargin cewa akwai alaka tsakanin gayyatar da tambayoyin da hukumar tsaro ta DSS ta yi wa Mailafia a kwanakin baya.

Ya ce DSS ce kada hukumar da dokar kasa ta ba wa hurumin binciken zargin da ke da nasaba da tsaron cikin kasa ba Rundunar ’Yan Sanda ba.

Tayar da kura

A kwanakin baya DSS ta yi wa Mailafiya tambayoyi bayan wata hira da aka yi da shi a gidan rediyo Nigeria Info inda ya yi zargin cewa wani gwamna mai ci a Arewacin Najeriya ne shugaban kungiyar Boko Haram.

Sauran zarin da ya yi a hirar kan yanayin tsaro a Arewacin Najeriya sun hada da cewa bakin ‘yan bindiga da Boko Haram daya kuma jiragensu na ta jigilar makamai da kudade a lokacin dokar kulle tamkar babu dokar.

Ya yi ikirarin cewa yana daga cikin wadanda suka gana da tubabbaun kwamandojin mayakan Boko Haram wadanda suka shaida masa haka, har ya ce ‘yan bindigar da suka bazu a ko’ina a Najeriya na shirin fara kai hari a cikin birane suna kashe manyan mutane, kuma za su fara yakin basasa a 2022.

Kalaman nasa dai sun haifar da muhawara da kiraye-kirayen a yi bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen tsohon Mataimakin Gwamnan na CBN.

Bayan fitowarsa daga ofishin DSS ya ce yana kan maganganun nasa da ko kafin nan sun sa an ci tarar gidan Nigeria Info tara.

Daga baya ya fito yana bayar da hakuri cewa ya ji abubuwan da ya fada din ne a bakin wasu mutane da ya hadu da su a kasuwar kauye.