✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maikaba ya fara aiki da Plateau United

Sabon Kocin kulob din Plateau United da ke Jos a Jihar Filato, Abdu Isa Maikaba ya fara aiki da kulob din a ranar Talatar da…

Sabon Kocin kulob din Plateau United da ke Jos a Jihar Filato, Abdu Isa Maikaba ya fara aiki da kulob din a ranar Talatar da ta gabata.

A lokacin da yake ganawa da sauran koci-kocin kulob din da kuma ’yan wasa a filin wasa da ke Hanyar Zariya a Jos ranar Talatar, Maikaba ya bukaci su ba shi hadin kai don ya samu nasara a kulob din.

Maikaba wanda tsohon Kocin kulob din Wikki Tourist da ke Bauchi ne, ya ce ta hanyar hadin kai da aiki tukuru daga wurin koci-kocin kulob din da kuma ’yan wasa za su sanya kulob din ya samu gagarumar nasara a kakar badi.

Maikaba wanda ya horar da kulob din Akwa United da ke Jihar Akwa Ibom, ya ce burinsa shi ne, ya lashe manyan kofuna biyu na cikin gida – na NPFL da na Aiteo, “Don haka burina zai cika ne idan ’yan wasa suka dage, sannan suka ba ni hadin kai. Na gamsu da ’yan wasan da na samu a Plateau United, zan yi aiki da su, kuma cikin ikon Allah za mu samu nasara, abin da nake bukata a wurinsu shi ne su ba ni hadi kai,” inji shi.

Kyaftin din kulob din Plateau United, Golbe Elisha ya yi wa Maikaba maraba da zama sabon kocin kulob dinsu, sannan ya tabbatar wa Maikaba cewa ’yan wasa za su ba shi dukan hadin kan da yake bukata don kulob dinsu ya kai ga nasara a gasar Firimiya  (NPFL) da ta Aiteo da za a fara.