✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Maigadi ya ki karbar kyautar gida ya nemi a yi wa kauyensa burtsatse

Wani maigadi ya ki amsar tayin kyautar gida a matsayin ladan ban-kwana da mai gidansa, dan kasar Indiya ya yi masa inda ya bukaci a…

Wani maigadi ya ki amsar tayin kyautar gida a matsayin ladan ban-kwana da mai gidansa, dan kasar Indiya ya yi masa inda ya bukaci a gina wa al’aummar kauyensu rijiyar burtsatse.

Mutumin mai Malam Musa Usman, dan asalin kauyen Giljimmi, wani matsugunin Fulani a Karamar Hukumar Birniwa a Jihar Jigawa, yana zaune ne a wani gidan kara a kauyen nasa.

Malam Usman, wanda ya yi aiki da mai gidansa, dan Indiya wanda Babban Manaja ne a Kamfanin Harhada Magunguna na duniya mai suna Jawa da ke Legas, ya ajiye aiki da mai gidan ne bayan ya shafe shekara 25 cur yana yi masa gadi, inda ya ce lokaci ya yi da zai koma gida wajen danginsa.

A lokacin da Malam Usman ya sanar da cewa zai bar aikin gadi, sai mai gidansa, Mista B. Berghese ya yanke shawarar ya gina masa gida a matsayin karamci kan irin kwazon da ya nuna lokacin da ya shafe a matsayin mai gadin gidansa.

Maimakon Malam Usman ya karbi wannan karamci, sai ya sa kafa ya shure batun gina masa gidan, inda ya nemi a gina wa kauyen na sa rijiyar burtsatse, saboda al’ummar kauyensa sun shafe lokaci mai tsawo suna fama da matsananciyar wahalar ruwan sha.

Al’ummar kauyen nasa sai sun yi tattaki mai tsawon gaske kafin su samu ruwan sha, sai yanzu an ’yanta su daga wannan wahalar ruwa ko shan ruwa marar tsabta, bayan da Ba’indiyen ya gina musu burtsatsen.

A tsokacin da ya yi, Malam Usman ya gode wa Mista Berghese kan irin wannan karamcin nasa, yana mai cewa ba ya nadamar sadaukarwar da ya yi ta rasa gida domin gina wa al’ummarsa rijiyar burtsatse ko kadan.