✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai yiwuwa a kwace gasar cin kofin Afirka daga Libya

kasar Aljeriya ta fara shirye-shiryen daukar nauyin gasar cin kofin Afirka a shekarar 2017 idan Hukumar shirya kwallo ta Afirka CAF ta kwace daga wajen…

kasar Aljeriya ta fara shirye-shiryen daukar nauyin gasar cin kofin Afirka a shekarar 2017 idan Hukumar shirya kwallo ta Afirka CAF ta kwace daga wajen Libya saboda tashe-tashen hankula da ake yi a kasar.
Shugaban Hukumar kula da kwallon kafa ta Aljeriya Mohammed Raoraroun ne ya shaidawa manema labarai haka a ranar Lahadin da ta wuce inda ya ce kasarsa tana da abubuwan da suka kamata don daukar nauyin gasar kama daga abin da ya shafi gine-gine irin na zamani da filayen wasanni da Otal-Otal da motocin sufuri da sauran abubuwan jin dadin rayuwa don haka yana da tabbacin kasarsa za ta iya duakar nauyin gasar a shekarar 2017 ba tare da wata matsala ba.
Shugaban ya ce Hukumar CAF ma ta yaba da abin da ta gani a kasa a lokacin da ta kai ziyara kasar a kwanakin baya a shirye-shiryen da hukumar ke yi na yiwuwar dauke gasar daga Libya zuwa Aljeriya.&nbsp Sai dai ya ce ya zuwa yanzu Hukumar ba ta yanke hukuncin ko za a yi gasar a Libiya ko ba za a yi ba sai a taron da za su yi a watan gobe.
kasar Libya ce dai aka amince za ta dauki nauyin gasar cin kofin Afirka a shekarar 2017 amma ganin yadda tashe-tashen hankula suka mamaye kasar ta sa Hukumar ta fara tunanin dauke gasar zuwa Aljeriya idan ba a samu daidaituwar al’amurra ba nan da wani lokaci.