✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kula da Kabarin Manzon Allah (SAW) ya rasu

An yi jana'izar mai kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Agha Abdou Ali Idris Sheikh

Allah Ya yi wa mutumin da ke kula da dakin da kabarin Manzon Allah (SAW) yake a Masallacin Madina, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, rasuwa.

Agha Abdou Ali Idris Sheikh, daya ne daga cikin mutanen da suka fi dadewa suna hidima a Masallacin Manzon Allah (SAW) da ke Madina.

Hukumar Gudanarwar Masallatan Harami ta sanar cewa, Agha Abdou Ali Idris Sheikh, ya koma ga Mahaliccinsa ne a ranar Litinin.

An gudanar da Sallar Jana’izarsa a Masallacin Manzon Allah sannan aka kai shi makwancinsa na karshe a Makabartar Baki’ da ke Makwabtaka da Masallacin Madina.

Abdou Ali Idris Sheikh shi ne Agha na uku da ya rasu cikin shekaru 10 da suka wuce.

A baya yawan masu aikin Agha ya haura mutum dubu daya, amma a halin yanzu wadanda suka rage a raye ba su fi biyar.