✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai kasada

Wani dan acaba ne ya biyo hanyar da ba ta dace ba, sojoji suka kama shi, suka sanya shi tsallen kwado. Bayan ya dade yana…

Wani dan acaba ne ya biyo hanyar da ba ta dace ba, sojoji suka kama shi, suka sanya shi tsallen kwado. Bayan ya dade yana yi sai aka sallame shi. Abin nan ya bata masa rai, lokacin da ya je zai buga babur, sai ya waiga ya ce masu: “Allah Ya isa!” Ya kama babur da sauri ya buga, babur ya ki tashi. Nan  take sai ya aje ya duka da tsallen kwado zuwa wajen sojojin.
Daga Usman Kawule 08052659678