✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mai ciki 1

Wani Bafulatani ne ya tafi da saniyarsa kasuwa, ya je tun da safe har yamma ba a taya ba. Ya dawo da ita gida sai…

Wani Bafulatani ne ya tafi da saniyarsa kasuwa, ya je tun da safe har yamma ba a taya ba. Ya dawo da ita gida sai matarsa ta tambaye shi cewa: “Ba ka sayar ba?” Sai ya ce: “Ko tayi ba a yi ba.” Sai ta ce: “Na ba ka shawara, idan ka koma ka ce tana da ciki.” Washegari ya koma kasuwa, yana zuwa sai wasu mutane suka ce masa za su sayi saniyarsa sai ya ce har ciki gare ta. Aka saye ta da daraja, ya zo ya fada wa matarsa, ya yi murna sosai. Wata rana kuma aka zo daurin auren ’yarsa, bayan shaidu sun zauna, za a soma daurin aure sai ya ce: “Gafarta malam, wannan yarinya fa mai daraja ce, har ciki ke gare ta!”