✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaukaci ne kawai zai ce a guji Atiku – Kwande

Tsohon Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, kuma dan Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar APC, Alhaji Yahaya Kwande ya ce mahaukaci ne kawai zai ce zai guji…

Tsohon Jakadan Najeriya a kasar Switzerland, kuma dan Kwamitin Amintattu na Jam’iyyar APC, Alhaji Yahaya Kwande ya ce mahaukaci ne kawai zai ce zai guji tsohon Mataimakin Shugaba kasa Atiku Abubakar.

Alhaji Yahaya Kwande, daya ne daga cikin wadanda suka kafa Jam’iyyar APC, sai dai a makon jiya ya sha suka da caccaka lokacin da ya yi wa Atiku rakiya zuwa Sakatariyar Jam’iyyar PDP ta Jihar Filato.

A yayin taron da aka shirya shi don Atiku ya gana da deliget din jam’iyyar ’yan jihar, Kwande ya yi jawabi, jawabin da bai yi wa jam’iyyarsa ta APC reshen Jihar Filato dadi ba, inda har ta kai ga rubuta masa wasika tana tuhumarsa da yi wa jam’iyyarsa zagon-kasa.

A cikin rubutaccen martanin da ya yi ga jam’iyyarsa, Yahaya Kwande ya ce ya halarci taron Atiku ne saboda alakar shekara 30 da ke tsakaninsu, kuma mahaukaci ne kawai zai ce ba ya tare da Atiku.

Yahaya Kwande a cikin wasikarsa ya ce “Duk da ni dan APC ne amma ina tare da Atiku, shi ne mutum mafi cancanta da ya dace ya shugabanci Najeriya, don haka duk wanda ya ce ba na tare da Atiku to mahaukaci ne.”

Ya kara da cewa a Jihar Filato ba ya da wani dan takara da ya wuce Gwamna Simon Lalong, kuma har yanzu bai fita daga Jam’iyyar APC ba, duk da cewa jam’iyyar ta mayar da shi saniyar ware duk da kasancewarsa daya daga cikin kwamitin amintattun jam’iyyar.