Wani mazaunin garin Dikwa a Jihar Borno ya ce mayakan da ake zargin na kungiyar Boko Haram ne da suka kaddamar da hari a garin a makon da ya gabata suna magana ne da wani yare ba irin na ’yan Najeriya ba.
Garin Dikwa, mai nisan kimanin kilomita 87 daga Maiduguri babban birnin Jihar, ’yan ta’adda sun kai masa hari ne ranar Litinin din da ta gabata bayan sun ci karfin sojoji sannan suka kore su daga garin.
- Jihar Neja za ta fara ba ’yan kato-da-gora bindigogi su yaki ’yan bindiga
- An rufe makarantu a Kwara kan takaddamar sanya Hijabi
Wani mazaunin garin wanda ya saurari maharan daga inda ya buya ya ce, “Lokacin da suke magana, wasu daga cikinsu na magana ne da yaren Kanuri, wasu daga cikinsu kuma na amfani da wani irin yare ne da ba irin na ’yan Najeriya ba.
“Sun ce za su jira wasu jami’an sojoji da suka nemi mafaka a wani ginin karkashin kasa sannan su yi musu yankan rago.
“Amma daga bisani ranar Talata sai wani ya shaida musu cewa sojoji sun yi jerin gwano sun tunkaro su, kawai sai suka cika wandonsu da iska,” inji majiyar.