✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Mahaifiyar Sarkin Kano ta rasu

Nan gaba za a sanar da shirye-shiyen jana'izar Mai Babban Daki.

Masarautar Kano ta sanar da rasuwar Hajiya Maryam Bayero, mahafiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

Hajiyar Maryam Bayero, wadda aka fi sani da Mama, ko Mama Ode, ta rasu ne a safiyar Asabar a wani asibiti da ke birnin Alkahira na kasar Masar.

“Allah ya yi wa Hajiya Maryam Ado Bayero rasuwa, mahaifiyar Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero.

“Za a sanar da lokacin jana’iza idan komai ya kammala,” kamar yadda Masarautar Kano ta sanar a shafinta na Facebook.

Sakataren Masarautar Kano, Awaisu Abbas Sanusi, ya ce Mai Babban Daki —mukamin da ake ba wa mahaifiyar sarki mai ci— ta rasu tana da shekara 86.

Marigayiyar ita ce kuma mahaifiyar Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero, kuma babbar matar Sarkin Kano, marigayi Alhaji Ado Bayero kuma ’yar sarkin a gidan Sarautar Ilorin.