✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiyar Sakataren Gwamnatin jihar Katsina ta rasu

A ranar Lahadin ce aka bayar da sanarwar rasuwar mahaifiyar Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Dokta Mustafa Inuwa. Kamar yadda Daraktan yada labaran Sakataren Malam Abdullahi…

A ranar Lahadin ce aka bayar da sanarwar rasuwar mahaifiyar Sakataren gwamnatin Jahar Katsina Dokta Mustafa Inuwa.

Kamar yadda Daraktan yada labaran Sakataren Malam Abdullahi Aliyu, ya ce a sanarwar da ya fitar, Hajiya A’isha wadda aka fi sani da Ta-Mashi mai kimanin shekaru 91 bayan tayi fama da jinya.

Hajiya Ta-Mashi ta rasu ta bar ƴaƴa 4 da jikoki 34. Daga cikin ƴaƴan da ta bari har da shi Sakataren gwamnatin Jahar Dokta Mustafa.

Tuni dai aka yi jana’izarta kamar yadda addinin musulunci ya tanadar.

A wani rahoto makamancin wannan, a yau ne wasu motoci biyu suka yi taho mu gama akan hanyar zuwa garin Jibiya da ke jihar. Rahotannin da muka samu na nuni da cewa, dukkan fasinjojin da ke cikin motocin sun kone, bayan arangamar motocin wadda aka ce daya na dauke da man fetur ne a cikin jarkoki yayin da motar daya ke dauke da karan rake.

Babu dai wani rahoto da ya fito a hukumance da ya baiyana dalilin aukuwar hadarin.