✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifiya ta binne jaririyar da ta haifa ranta a cikin masai

Ana zargin ta kashe jaririyar ne bayan ta haife ta a sanadiyar cikin shege

An kama wata mata mai kimanin shekara 30 da ke kauyen Tsurma a Karamar Hukumar Kiyawa ta jihar Jigawa bisa zargin binne jaririyar da ta haifa a cikin masai.

Da yake tabbatar da kamen, Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Lawan Shi’isu, ya ce tuni suka tono gawar jaririyar sannan suka cafke wacce ake zargin.

Ya kuma ce, “Bayan samun rahoton, mun aike da jami’anmu zuwa wajen, inda suka tono gawar daga cikin masan da ake zargin a ciki ta binne jaririyar.

“Yanzu haka mun cafke matar kuma tana hannunmu,” inji Lawan.

Kakakin ya kuma ce an garzaya da gawar Babban Asibitin Dutse, inda likita ya tabbatar da rasuwarta.

Ya kuma ce bincikensu na farko-farko ya kai su ga kama wani mai suna Amadu Sale da aka fi sani da Dan Kwairo mazaunin kauyen Akar a Karamar Hukumar ta Kiyawa, wanda shi ake zargi tun farko da yi mata cikin shege.

Ya ce bayan yi mata cikin, an zargi Dan Kwairo da hada baki da ita domin ta kashe yarinyar bayan ta haife ta.

Kakakin ya kuma ce tuni Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Emmanuel Ekot, ya ba da umarnin mayar da lamarin zuwa sashen binciken manyan laifuka na rundunar domin fadada bincike.

Ya ce da zarar an kammala binciken, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kuliya domin su girbi abin da suka shuka.