✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mahaifina mutum ne mai barkwanci da tarbiyya – Hadiza Buhari

Hadiza Buhari ita ce ta hudu a ’ya’yan Janar Buhari mai ritaya, wanda ya taba shugabancin kasar nan, kuma a yanzu shi ne dan takarar…

Hadiza Buhari ita ce ta hudu a ’ya’yan Janar Buhari mai ritaya, wanda ya taba shugabancin kasar nan, kuma a yanzu shi ne dan takarar shugaban kasa nan a jam’iyyar APC. A hirar da ta yi da Aminiya ta yi bayanin yadda mahaifinta ya zama gwarzon al’umma da sauran al’amura. Ga yadda hirar ta kasance:

Aminiya:Ya ya kika taso kasancewarki ’yar mashahurin Janar din soja?
Hadiza Buhari: Na taso kamar kowa. Mahaifina yakan fada mana ni da ’yan uwana, cewa, rayuwa fa ba ta da tabbbas. Ina da kawaye da yawa ‘ya’yan masu hali, wadanda na yi sha’awar zama kamar su, ta wajen sayen kaya masu tsada da sauransu, da ya lura da haka, sai wata rana ya kirawo ni, ya ce ‘kin san na sayar da kadarorina domin in biya muku kudin makaranta ko?’ Tun daga wannan lokaci na shiga taitayina. Saboda haka muna rayuwarmu kamar kowa, mukan je kauye, har ma gona ya rika zuwa da mu.
Aminiya:Wane irin uba mahaifinki ya kasance?
Hadiza:Ya kasance mahaifi mai nuna kauna, har ta kai har yana taimaka mana da aikin makaranta. Akwai abubuwan da nake tunawa da yawa, a shekarar 1990 lokacin damuna, ni da kanwata muna so mu ga ruwan kankara, sai ya lallabo ya shiga kicin ya debo guntattakin kankara ya rika watso mana. Sai mu yi ta murna mun zata ruwan kankara ne da gaske. Abin ya yi mana dadi har bayan da muka gane.
Lokacin da dan uwansa ya rasu a shekarar 1987, sai ya dauki nauyin ’ya’yansa guda bakwai. Haka nan ya dauki nauyin ‘ya’yan marigayi Sarkin Nassarrawa Alhaji Abubakar. Yana da kulawa sosai.
Aminiya: Wace irin kuruciya kika yi a gabansa da ba za ki iya mantawa da ita ba?
Hadiza: Cin abinci tare da shi. A da matukar yana gari tare muke cin abinci, tun bayan da na yi aure sama da shekaru 11 na daina samun wannan damar.
Haka nan na yi rashin rakiyar da yake yi mana zuwa makaranta. Bayan mahaifiyarmu ta fita, shi ne yake yi mana komai. Sai ya zama shi ne tamkar mahaifiyarmu, inda ya rika tashinmu don shirin tafiya makaranta. Muna karin kumallo yana sauraron labaran BBC ko Muryar Amurka. Idan ya ga mun shiga mota, saboda muna da yawa sai ya ce ”Kabo Air a dawo lafiya”.
Aminiya:Wane halinsa ne ya fi tasiri a gare ki?
Hadiza:Ya kasance mai tsayawa a kan gaskiya ko da yaushe, saboda haka nake kokarin ganin ‘ya’yana ko da yaushe su ma sun zama masu gaskiya. Muna yara idan muka tambaye shi kwabo biyar domin mu sayo alewa, sai ya ba mu kwabo 50, idan ba ka ba shi canji ba, sai ya ce mana ya kamata mu dawo da canji kafin a tambaye mu. Yakan ce mana kada mu kuskura mu rike kudi ko kayan wani a wurinmu, na dora yarana a wannan tafarkin nima.
Na koyi taimaka wa ‘ya’yana wajen tabbatar da cewa sun kammala, aikinsu na makaranta. Da, mukan yi layi ya taimaka mana da aikin makarantarmu daya bayan daya.
Aminiya: Ko kina fuskantar matsin lamba saboda ke ‘yar Buhari ce?
Hadiza: A gaskiya babu. Mutane suna yi mana kallo daban, amma da zarar sun yi hulda da mu, sai su ga muna da saukin kai. Muna yawonmu ba tare da mutane sun sani ba. Amma yanzu, abin ya canza.
Aminiya: Da mahaifinki ba soja ba ne ko dan siyasa, da mai kike ganin zai fi kwarewa a kai?
Hadiza:Ina ganin da ya zama babban manomi, don ya iya kiwon shanu, har rakuma ya taba kiwatawa, amma yanzu ya rabu da su.Yana da wani wuri da ya shuka mangwaro a ciki. Don haka nake ganin da ya zama babban manomi.
Aminiya: Kina ganin a gida ma yana nuna halayyar soja?
Hadiza:A gida yana da saukin kai, yana wasa da mu, amma fa wajen tarbiyya ba wasa. Muna da yawa don haka dole ya ja damara, domin kada mu sangarce. Wani lokaci idan ya kalle mu, ba sai ya yi magana ba, mutum zai nutsu.
Aminiya:Wane abinci babanki ya fi so?
Hadiza:Yana son tuwon alkama da miyar kuka, kuma yana son sakwara. Amma saboda lafiyarsa sai ya fara daidaita abin da zai ci. Kuma yana son kayan marmari sosai.
Aminiya:Mene ne aka fi sani game da mahaifinki?
Hadiza: Ana yi masa kallon mutum mai tsanani, amma yana da son barkwanci, har ya kyakyata dariya sosai.Wani lokaci mun je Ingila hutu, gidan da muke bene ne, kuma dakunan kwana suna kasa, dakin shakatawa kuma yana sama.Ina saukowa daga sama sai na sunbule na fodo gaban dakinsa. Sai ya fito da sauri yana addu’a ya zaci wani abu ne ya fado, kawai sai ya ganni, sai ya tuntsire da dariya ya ce ‘ba za ki manta wannan ba har ki girma.’
Aminiya: Ko akwai wata rashin fahimta akan mahaifinki da kike son fito da gaskiyar lamarin?
Hadiza: Al’amarin da yana cike da mamaki yadda mutane ke daukarsa a matsayin mai tsaurin addini. Ina so su daina yi masa wannan kallo, kuma su daina danganta shi da wannan. Mahaifina da sauran ‘yan gidanmu muna da kyakkyawar mu’amala da mutanen da ke yi bin wani addini daban. Da haka ne, da ya tura mu ni da kanwata kasashen addinin Musulunci mun yi karatu, amma bai yi haka ba. Na so in karanta harsunan Larabci da Faransanci a kasar Saudiyya ko Masar, amma ya dage sai da na tafi Ingila.