✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magu ya kalubalanci Malami ya bayar da shaida kan bincikensa

Ya kalubalanci Ministan Shari'a ya gabatar da takardun da ke tabbatar da zargin da yake masa

Dakataccen Shugaban Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziki Ta’annati (EFCC), Ibrahim Magu, ya bukaci kwamitin da Shugaban Kasa ya nada ya bincike shi da ya gayyaci Ministan Shari’a, Abubakar Malami.

A wasika da lauyansa, Wahab Shittu, ya sa wa hannu, Magu ya ce Malami ya zo ya gabatar da shaida tare da muhimman takardu kan takardar zargin da ya gabatar wa Shugaban Kasa a kansa.

Wasikar Malamin ta kunshi cewar: “Mukaddashin Shugaban Hukumar EFCC ba ya gudanar da aikinsa bisa kishin kasa ko manufofin shugabanci kasa, la’akari da wadaka da rashin gaskiya da ake yi da dukiyoyin da ake kwatowa a hannun barayin gwamnati; canja akalar dukiyar da aka kwato; son azurta kai; kin mayar da hankali wajen bincikar rikicin P&ID kamar yadda shugaban kasa ya umarta da kuma kin bin umurnin kotu”.

Da wakilinmu ya tuntubi Mai Magana da Yawun Ministan Shari’a Dakta Umar Gwandu, sai ya ce Malami ba zai yi tsokaci kan maganar ba saboda har yanzu tana gaban masu binciken na shari’a.