Wasu daga cikin magoya bayan kulob din Real Madrid na Sifen a ranar Lahadin da ta wuce ne suka huce haushinsu ta hanyar farfasa gilashin motar daya daga cikin ’yan kwallon kulob din Gareth Bale jim kadan bayan kulob din FC Barcelona ya lallasa na Real Madrid da ci 2-1 a gasar rukunin La-Liga na Sifen.
Bale, wanda shi ne dan kwallon da ya fi kowane tsada a fadin duniya, bayan da Madrid ta saye shi a kan Fam miliyan 86 ko Yuro miliyan 100 ya gamu da fushin wasu daga cikin magoya bayan kulob din ne saboda rashin tabuka abin a-zo-agani a wasan, al’amarin da ya sa kulob din ya cigaba da kasancewa na biyu a rukunin La-Liga bayan da Barcelona ta ba shi tazarar maki hudu.
Rahoton ya ce jim kadan bayan Gareth Bale ya fito daga filin wasan ne ya gamu da fushin wasu daga cikin magoya bayan kulob din inda suka rika zaginsa ta-uwa-ta-uba yayin da wasu suka far wa motarsa da bugu da jifa kuma suka farfasa masa gilashi.
Sai dai tuni kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid ta nuna bacin ranta a kan wannan al’amari kuma ta sha alwashin gudanar da bincike don hukunta wadanda suka yi wannan aika-aika.
A washegari ne kuma watau a ranar Litinin da ta gabata, wasu daga cikin jaridun Sifen suka caccaki Gareth Bale a shafin farko na jaridunsu. Yayin da jaridar AS ta ruwaito cewa Gareth Bale bai samu maki ko daya daga cikin 10 da ta dora shi a bisa sikeli ba ita kuwa jaridar Marca cewa ta yi akwai takaici ganin yadda Shugaban kulob din Madrid Florentina Perez ya sayo Bale a kan Yuro miliyan 100 maimakon Yuro miliyan 20 ganin yadda kwalliya ba ta biya kudin sabulu ba.
Sai dai ajent din Gareth Bale ya ce dan kwallon yana nan daram a Madrid, hasalima bai da niyyar barin kulob din a halin yanzu ba, duk da irin sukar da yake samu daga bangarori da dama.