Wani abu mai kama da almara ne ya faru a garin Dirin Daji a Jihar Kebbi, inda wani mutum ya maka dan uwansa a kotun saboda abinci.
Wani mazaunin garin mai suna Murtadha Faruk Sale ya tabbatar wa wakilinmu cewa hakan ta faru a garin, inda ya zayyane masa abin da ya faru kamar haka:
“Wannan wa ne da kanensa, shi wan babu abinci gidansa, tun da kanensa nada abinci ya fi karfin abin sai ya je gidan kanen ya tambayi matarsa ina dan uwan nasa yake, ta ce ba ya nan.
“Shi kuma sai ya gaya wa matar kanen ga halin da ake cikin gidansa na rashin abin da za a ci, sai matar kanen ta shiga da auno kwano 10 na hatsi taba shi ya tafi.
“Koda mijin ya dawo sai ta kwashe yadda ta yi da yayansa; to wannan abu sai ya bakanta wa mijin rai, sai ya nufi kotun majistare ya kai kara.
“Sai alkali ya aika masa da sammaci, koda ya zo, alkali ya tambaye shi, ya sa aka binciken shi, aje gidansa a duba idan akwa abinci ko babu a dawo a gaya wa kotu.”
Murtadha Faruk Sale ya ce haka haka alkala ya sa aka yi a gidan kanen.
“Ko da aka je gidan kanen an iske buhunan abinci za su kai 50, aka dawo aka gaya masa, alkali ya ce to a koma a kwaso buhu 5, aka je aka kawo.
“Sai nan take alkali ya ba da umarni a sayar da buhu daya, aka sayar sai ya yanke hukunci a ba dan uwan da aka kawo kara kudin huhu dayan, a hada ma sa da buhunan hudu da kudin a ba shi.
“Sannan ya ja kunnen kanen cewa ko kusa kada kotu ta samu labarin ya ci zarafin matarsa a kan haka,” in ji shi.