✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Magidanci ya kashe diyarsa saboda talauci

Wani mutum ɗan asalin ƙasar Benin, wanda ke zaune a garin Abekuta a jihar Ogun ya halaka ’yarsa ’yar wata 6 da haihuwa. Mutumin mai…

Wani mutum ɗan asalin ƙasar Benin, wanda ke zaune a garin Abekuta a jihar Ogun ya halaka ’yarsa ’yar wata 6 da haihuwa.

Mutumin mai suna Kofo Andrew, ya shaida wa Aminiya cewa fatara da talauci da kuma rasa yadda zai yi da ’yar wacce ita ce ’ya ɗaya tilo da matarsa da yake zaune da ita ta haifa masa, sakamakon ƙaurace masa da ta yi. “A ƙarshen watan jiya ne sai matata ta bayyana mani sabbin halaye waɗanda ban santa da su ba, sai na fahimci cewa mahaifiyarta ce ta hure mata kunne, ta ce ba za ta yi aure da ni ba. Daman can ba mu kai ga yin aure ba, muna zaman ‘wajoko’ ne da ita har ta haifa mani yarinyar. To, ganin yadda mahaifiyar take hure mata kunnuwa sai ta ajiye mani yarinyar, ta tafi abinta. Hakan ne ya sanya na ɗauke ’yar tawa na kai wa mahaifiyata, domin ta ba ta kulawa. Mahaifiyar tawa ta riƙe ta na tsawon mako guda daga nan ta nuna gajiyawarta da riƙon nata, ganin irin yanayi na halin rashin kuɗin da nake fama da su, ba na iya ba ta wani abin kirki, domin sana’ar aski da noma nake yi, sai na koma wajen matar tawa na lallaɓe ta da ta dawo ta ci gaba da bai wa ’yar tamu kulawa. Koda ta dawo ta yi kwana ɗaya sai ta sake bijire mani, ta nuna cewa ba za ta iya ci gaba da zama ba, bayan na rarrashe ta taƙi yarda sai na shaida mata cewa muddin ta tafi, to zan kashe ’yarinyar.  Ba ta saurare ni ba, da ta tafi abinta sai na ɗauko adda na datse ’yar tamu gida biyu,” inji shi.

Mutumin da ake zargi da kashe ’yar tasa ya ƙara da cewa, a gaban mahaifiyarsa ya kashe ’yar tasu, ba kuma ta yi yunƙurin hana shi ba. “Ko da matar tawa ta tafi na yi ƙoƙarin ganin mahaifiyata ta sanya baki, domin samun daidaito sai ta yi biris, ta ce babu ruwanta. Ganin hakan ne na sanya adda na raba ’yar tamu gida biyu, na kashe ta ne a ɗakin mahaifiyata. Na kuma yi nadamar aikata hakan, don haka ban nemi tserewa ba har sai da mai unguwarmu ya sanar da ’yan sanda suka kama ni, “inji shi.

Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya shaida wa Aminiya cewa wanda ake zargin ya tabka mummunan laifi domin laifin da ya shafi ɗaukar ran ɗan Adam ba ƙaramin abu ba ne. “Ai ko kaza idan ka ga ta take ɗanta, tana yin haka ne domin gyara ɗan, shi ko wannan da yake she ’yar cikinsa don gudun talauci, a yanzu ne ma zai fara ganin talauci tun da ya shiga hannunmu.” Inji Kwamishinan, wanda ya ƙara da cewa rundunar na ci gaba da bincikar lamarin, kuma za a gurfanar da wanda ake zargin da zarar an kammala bincike.