Tsohon Kwamishinan harkokin addini na Kano Dokta Muhammad Tahar Adamu (Baba Impossible) ya ce muryarsa da ke yawo a kafafen sada zumunta kan ba a yi wa Sheikh Abduljabbar Nasir Kabara adalci ba, daliban malamin ne suka saki don bata masa suna.
A tattaunawarsa da gidan rediyan Freedom da ke Kano, Baba Impossible ya ce kalaman da ake zarginsa da furtawa, yayi su ne tun a baya, a wani shirin gidan rediyon Kano na gwamnati.
- Fasto ya sace kansa ya karbi kudin fansa daga mabiyansa
- Maigidanci ya nemi matarsa ta biya shi N320,000 a madadin aurensu
“Yadda kowa ya ji muryar nan nima haka aka turo min, amma fa yanko farko aka yi, aka hada da karshe saboda a bata ni a gun mutane,” in ji shi.
Muryar dai ta fara karade kafafen sada zumunta da tada kura ne bayan Kotun Shari’ar Musulunci ta jihar ta yanke wa malamin hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Cikin muryar dai, an jiyo Baba Impossible din na cewa ba don kare martabar Annabi (S.A.W) malaman suka yi mukabala da Abduljabbar ba, kuma ko shakka babu gwamnatin Kano ba ta yi masa adalci ba.
Haka kuma a cikin muryar, Baban ya ce batun batancin da aka zargi Abduljabbar DIN da shi a wancan lokacin, kwangila ce daga wasu kasashen waje, da kuma wasu malaman Kano masu akidu daban-daban, da malamin ya taba mutuncinsu.
Baba Impossible ya kuma ce muryarsa da aka ji a ciki yana cewa malaman da gwamnati ba su yi wa Abduljabbar adalci ba, martani ne ga wani dalibin malamin da ya kira shi a waya yana zarginsa da zaluntar malaminsa.