Matar nan da ta auri saurayin ’yarta a Jihar Kano, Malama Khadija ta jadadda cewar ba za ta sauya ra’ayinta ba duk da cece-ku-cen da jama’a ke yi a kanta, tun da ba ta saba wa Allah ba.
Aminiya ta ruwaito yadda mutane da dama suka dinga mamakin yadda uwa ta aure saurayin ’yarta, wasu kuma suka kasa gasgata lamarin.
- NAJERIYA A YAU: Yadda ’yan Najeriya suka karbi karin wa’adin tsoffin kudade
- Masu garkuwa sun bukaci babura da kayan abinci a matsayin fansa a Kaduna
Idan za a tuna, Khadija ta bayyana dalilin da ya sa ita da ’yarta suka amince kan kada su rasa saurayin duba da wasu tarin halaye masu kyau da ta ce yana da su.
Kazalika, ta bayyana dalilin da ya sa ta kashe aurenta sannan ta auri matashin.
Ta ce, “Ina mamakin yadda mutane suka sa aurena a gaba. Ni na yanke hukunci da kaina. Babu wanda ya min dole. ‘Yata ta ce ba ta son shi, ni kuma na ga ba zai yiwu mu rasa shi ba. Muna zaman lafiya kuma ina jin dadin zama da shi.
“Ina so mutane su sani sai da na tambayi Malamai game da auren nan kuma suka ce min babu wata matsala zan iya yi, saboda haka ba sauya ra’ayina a kan auren nan ba. Na zo don na zauna kuma ba na bukatar shawarar kowa,” in ji ta.
Game da zargin da ake yi wa Kwamandan Hisbah na Karamar Hukumar ta Rano kuwa, Khadija ta ce ba shi ya mata dole kan auren ba.
Kazalika, hukumar Hisbah ta Jihar ta ce tuni ta kafa kwamitin da zai binciki lamarin.