Ministan Lantarki, Injiniya Sale Mamman ya bayyana labaran da ake yadawa a kan yuwuwar kara kudin wutar lantarki a matsayin na kanzon kurege.
Ya ce ko daya gwamnati bata da wata aniyar kara kudin a yanzu.
- Auwalu Daudawa: An harbe mutumin da ya kitsa sace Daliban Kankara
- A wata uku an kashe mutum 323, an sace 949 a Kaduna
Ministan, wanda ya ba da tabbacin a cikin wata sanarwar da fitar ranar Juma’a ya ce a maimakon karin kudin, ’yan Najeriya su tsammaci ingantuwar wutar da kuma rage yawan kudaden da ake caza daga hannunsu nan ba da jimawa ba.
Tabbacin na zuwa a daidai lokacin da rahotanni suka karade gari kan yuwuwar yin karin a kan kudin wutar da ake biya yanzu.
Mamman ya ce umarnin da Hukumar Kayyade Farashin Wutar Lantarki ta Kasa (NERC) ta bayar ranar 26 ga watan Afrilu da yake sanar da karin kudin dama a kan yi shi duk bayan watanni shida, ko da yake bai shafi jama’a kai tsaye ba.
A cewarsa, “Har yanzu kwastomomin da suke kan Layukan D da E (wadanda ke samun wutar ta kasa da sa’o’i 12 a kowacce rana) za su ci gaba da biyan farashin da ake sakawa tallafi kamar yadda Gwamnatin Tarayya ta ba da umarni.”
Injiniya Sale ya kuma ce gwamnatinsu ta damu matuka wajen ganin ta kawo karshen matsalar lantarkin da ta jima tana ci wa ’yan Najeriya tuwo a kwarya ta hanyar samar da kayayyakin aiki ga kamfanonin rarraba hasken wutar a Najeriya.