✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mafitar Najeriya a 2015

Edita ka ba ni dama in tabatar wa ‘yan Najeriya, cewa, zaben 2015, zabin Allah ne mafita ga al’umma. Tabbas babu mai hankali da zai…

Edita ka ba ni dama in tabatar wa ‘yan Najeriya, cewa, zaben 2015, zabin Allah ne mafita ga al’umma. Tabbas babu mai hankali da zai ga wannan farkon magana ya ce da ni sam !!!
Domin da masu bukatar samun sauyi, da masu neman ta zarce duka muna cewa, mulkin adalci muke so, amma muna kauda kai ga matsaloli da hanyar kauda su,har kullum kai bawa ka ba Allah zabim da neman mafita ta hanyar dogaro agareShi. A kawar da kabilanci da kallon duk wata jam’iyya a nemo, tare da addu’ar samun managartan mutane, ba masu halin ramin kura ba. Kai mu dubi irin halin rashin tsaro a Arewa maso Gabas.  Allah ya azurta kasarmu da adalan shuwagabanni,
Daga Mukhtar Ibrahim Saulawa Katsina, 07066434519.08080140820.

Addu’a ga kasa
Edita ka ba ni dama in yi addu’a ga daukacin al’ummar Najeriya, Kirista da Musulmi, mu dage da addu’ar neman zaman lafiya. Daga 08031944943.

Ga Sarkin Malaman Katagum
Edita ka isar min da sakon gaisuwa ga Maigirma Sarkin Malaman Katagum, Alhaji Alkali Mahmud. Da fatan Allah Ya ja kwana da koshin lafiya. 07038654650.

Jinjina ga Editan Aminiya
Jinjina da yabo mara adadi ga Editan Aminiya. Daga Isah Sani Mai Arsenal 08072556844.

Godiya ga gwmanatin Kano
Edita ka ba ni dama in yi godiya ga Gwamnatin Jihar Kano kan gine-gine da gyare-gyaren makarntu da ake yi mana. Mun gode kuma za mu yi murna idan aka tuna da SAS. Daga 08034507166.

Ga Baba Buhari
Zuwa ga Baba Buhari, lallai ka fito takarar shugaban kasa. Allah Ya yi mana zabi mafi alkhairi. Daga 08079156747.

Ga APC a Katsina
Aminiya don Allah ku mika min sakon taya murna ga ’ya’yan jam’iyyar APC na Jihar Katsina, bisa kamun da muka yin a jigon PDP a Katsina. Hon Sani abdullahi Dabai zuwa APC. Daga Musa Unguwar Maiyasin, danja, Jihar Katsina 08060611124.

Ga Aminiya
Editan Aminiya, ina so ka ba ni dama in yi yabo da jinjina ga jaridar Aminiya, kan tsage gaskiya. Allah Ya kara muku basira da farin jini da daukaka. Daga kasimu  08034376194.

Wasikar Obansanjo
Edita wasikar Obasanjo na neman tabbata, don haka kowa ya shiga taitayinsa, musamman ma ind aya zargin Jonathan d ahorar da wsu amtasa wadanda za su akshe wau dattawa. Yau dai kun ga jirgin Orijisafor ya tafi sayen makamai a Afirka ta Kudu.to ina Dattawan Arewa? Allah Ya ba mu mafita. Daga Isa Sani.

Ga talakawan Nasarawa
Ina kira ga talakawan Jihar Nasarawa da su ci gaba kare mutuncin gwamnanmu, Alhaji Umaru Tanko Al-makura. ‘’Yan majalisa ku tuba, ku bi gaskiya, talakawa bas a tare da ku. Allah Ya akre Al-makura. Dag Alhaji 08085858888.

Rikici a Afirka
Edita ka ba ni dama in nuna takaicina game tashe-tashen hankula a kasashen afirka, musamman a kasata Najeriya. A gaskiya wadannan tashe-tashen hankulan da ake fama da su, a wasu kasashen  Afirka, to suna da alaka da rashin shugabanci nagari. Dalili shi ne, za ka ga mutun yana matsayin shugaban kasa, amma kasarsa ana fama da talauci da yunwa, ga rashin aikin yi, ga matasa, ga kuncin rayuwa da jama. Kuma dukkan wadannan abubuwan akwai yadda za. A yi a magancesu, amma saboda son zuciya da zalunci, an yi wai kuma a haka kana so kasarka ta zauna lafiya, to, ya ya za a yi a zauna lafiya ana zaluntar jama?
Daga Ababakar Lawal Gidan Danmaye a Jargaba, karamar Hukumar Bakori, Jihar Katsina Najeriya +2348097627776.

Abin Kunya Ga Gwamnatin Tarayya
Editan Aminiya, amsar mallakar Dala miliyan tara da dubu 300 da Gwamnatin Tarayya ta yi, abin kunya ne ga Najeriya. Kuma yin hakan ya haska wa duniya gaskiyar zargin da ake yi wa gwamnatin, na daukar nauyin ayyukan ta’addanci da daure wa masu cin hanci da rashawa da masu aikata laifi gindi.
Daga Mansoor Said PRP Kano . 07039215954.

Ana tauye kuratan soja
Edita laifi tudu ne, ka take naka ka hango na wani; na fadi hakane ganin yadda sojojin Najeriya  ke korafin ana tauye musu hakkinsu, a wajen aiki, amma aka ki kula su sai da ta kai ga har sun yi bore, sannan ne aka kama su aka kai su kotu, aka yanke musu hukuncin kisa. Su kuma manyan da suke zaluntarsu  ko a jikinsu;  shi ke nan su ba za a bincikesu ba?  Mie ya sa suka tauye hakkin kuratan sojojin su ba?
Daga Usman Adamu aliero, Kebbi, 07061594299

Ga ’yan majalisar Arewa
Idan  ’yan  majalisun  Arewacin  ba su dauki  wani  kwakkwaran mataki ba  akan  Shugaban  Kiristoci na  CAN  ba,  Musulmi  na daf da fadawa  kisan  kiyashi,  masamman  a  Arewa  maso  Gabashin  Najeriya. Jirgin Orijisafor mai dauke da kudi shirin cutar da ’yan Najeriya ne
Daga  Garba  Sabiola  Gashu’a  08096284154.

A tsayar da Buhari
Edita na yi kira ga shugabannin jam‘iyyar APC na kasa, da su fitar mana da jagoran talakawa, Janar Muhammadu Buhari, a matsayin dan takarar shugaban kasa, a karkashin jam’iyyar APC. Domin babu wanda ya kamata a tsayar takara kamar Janar Baba Buhari. Don haka mu talakawa Janar Baba Buhari muke fata ya fito mana takarar shugabancin Najeriya, don kawar da mulkin zalunci, da kama karya na jam’iyyar PDP. Daga Isah Ramin Hudu, Hadejia. 08060353382.

Tutar Lawal Jafaru Isa
Edita a fada wa Kanawa, don Allah su daga mana tutar Lawal Jafaru Isa a Kano, ta yadda za a ci gaba da aiwatar da managartan ayyuka da adalci a tsakanin al’umma. Uwa kaka barka, Lawal Jafaru Isa ya dau tuta. Allah Ya yi mana zabi managarci. Amin. Daga Ahmad Tiga.

Batun sayen makamai
A bincika batun batun sayo makamai a Jirgin Shugaban kungiyar CAN. Ina shawartar shugabannin arewa da kada su yi sakaci. Allah Ya tsare mu daga sharrin masu sharri. Daga  080876885710.