✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Mafita daga rikicin Boko Haram

Editan Aminiya ka ba ni dama in gabatar da shawarata kan neman mafita daga rikicin Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci da suka dabaibaye Arewa,…

Editan Aminiya ka ba ni dama in gabatar da shawarata kan neman mafita daga rikicin Boko Haram da sauran ayyukan ta’addanci da suka dabaibaye Arewa, musamman a Jihohin Barno da Yobe. Allah Ya kawo wa al’ummar Yobe da Barno mafita daga bala’o’in kisan gilla. Sai dai al’umma a sani Allah ba Ya sauya halin da mutane ciki har sai sun sauya da kansu. Mu kiyaye haddodin Allah, mu martaba kur’ani, mu daina tsibbace-tsibbace; mu bai wa ’ya’yanmu tarbiyya. Mu daina banga da dabar siyasa. Mu yi karatun zamani da na addini; sai kuma noma da kiwo da kasuwanci, kamar yadda Shehu Mujaddadi ya yi mana wasiya. Wannan ita ce maslaha. Wanda duk yake aikata ayyukan ta’addanci, Mai da’awar Musulunci ne ko mabiyin wani addinin, kada mu goyi bayansa, ko da a zukatanmu ne, don Allah Ya jibinci lamurranmu. Allah Ya sa mu dace.

A dawo da Dausayin kauna
Salam. Aminiya ba ku yi wa masoya adalci da kuka rufe shafin ‘Dausayin kauna,’ ba, yau shekara guda ke nan. Ya kamata ku dawo mana da shi kwana nan. Daga Husnah Dabai 07068514071.

Barace-barace a Arewa
Barace-barace ya addabi Arewa, har ya jawo rashin tarbiyya da ta damu jama’a, saboda ’ya’ya ba su tashi a gaban uwa da uba ba. Wasu ba su san darajar manya ba. Don Allah manya a yi kokarin mayar da yara garuruwansu, a tanadar musu kulawar iyaye da wuraren neman ilimin zamani da na addini. Daga 07053539334.
 
An manta da masu faskare
Aminiya ba ku taba hira da mai faskare ba. Kuma ku gaya wad an majalisar Funtuwa Rabi’u Dos ya manta da makwaftansa, masu yin faskare. Daga Murtala Dogon Yaro Funtuwa 08039374146.
 
Gaisuwa ga Kwankwaso
Editan Aminiya muna tare da ku a kodayaushe, don Allah ka mika min gaisuwa ga Gwamna, Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso mai dubban Masoya. Daga Ameena Giginyu 08187393510
 
Udojin kudin Abacha
Ina mai ba Shugaban kasa shawara kan ya debi kudin Marigayi Janar Abaca da aka ce an karbo, a yi wa ’yan Najeriya Udoji da su, ko ya bar abin tarihi. Daga Garba Shugaban kungiyar Dogaro ga Allah Hutu na Jihar Katsina 08166283568.
 
Ga Shekau
Jaridar Aminiya ki fada wa Shekau idan ya kashe mutanen da ya lissafo, shi kuma sai ya zauna jiran duniya. Daga Mahmoud Jos 08088573200.
 
 Allah Ya kawo mana karshen ta’addanci
Innalillahi wa inna ilaihir raji’un. Ya Allah Ka kawo mana karshen wannan kisan gilla da ta’addanci a jihohinmu na Yobe da Barno da Adamawa. Daga Umar M. Baba Gashua 08074141220.
 
Haba Gwamna Shema
Wai ina maganar zaben kananan hukumomi ne? Aminiya a tunatar da Mai girma Gwamna Shema, mun gaji da gafara sa, ba mu ga kaho ba. Don Allah a yi mana zabe ko talauci ya ragu ga al’umma. Daga Nasir Balarabe Dankama (Nasko) 07050584990.
 
Ga Mataimakin Gwamnan Katsina
Aminiya, muna godiya ga Alhaji Abdullahi Faskari kan biyayya da hadin kan da yake ba Gwamna Shema mai albarka, don Jihar Katsina ta kara zama uwa ga sauran jihohin kasar nan, wajen zaman lafiya da ci gaba. Daga Amiru Isa Bakori 08075959086.
 
Gaisuwa ga Gwamna Gaidam
Asssalamu alaikum. Edita Aminiya a mika min gaisuwa ga Gwamnanmu Alhaji Ibrahim Gaidam na Jihar Yobe. Muna godiya saboda samar mana aiki mu matasan Jihar Yobe. Jinjina ga jagoran APC na Jihar Yobe. Gaba ta fi baya yawa. Daga Adamu AC Potiskum Dogo Teobo Word 08137084458.
 
Nawa ne kudin sako?
Salam, zuwa ga Editan Aminiya. A fada mini idan kudi ake bayarwa. A fada min in biya, indai na turo sako ba a buga ba. Daga Ummah Usman Kano 08099834011.
 
Shekarau ya koma gida
Salam Aminiya ku gaya wa Malam Ibrahim Shekarau da ma mutane suna zarginsa da cewa dama dan PDP ne, don yanzu ya ce ya shiga PDP ai babu mamaki, dama gidansa ne. Allah raka taki gona. Daga Adamu Suleiman Kaugama 08057672400.
 
Kira ga Gwamnan Jihar Kaduna
Kira ga Gwamnan Jihar Kaduna. Don Allah Ya kafa kwamitin bincike a wuraren da aka yi kashe-kashe da ji wa mutane rauni, tun da ya ce shi mai tausayi ne. A ziyarci Zonkuwa da Kafachan da kaura, a duba wadanda rikici ya shafa, da masu “raunin harsashi, a fadan da aka yi lokacin shagalin dmas. Nagode. Daga 07053539334.
 
Ta’aziyyar APC
Editan Aminiya mun yi murna da babban taron jam’iyyarmu ta APC, musamman ganin yadda masu kishin jam’iyyarmu suke kokarin kawo sauyi. ’Yan forum dinmu ta kishin jam’iyya da Najeriya, muna yi wa Umar Jibo, Sakataren tsare-tsare na kasa ta’aziyya saboda rasuwar mahaifinsa. Daga Lawal Abubakar baure 07060792797.
 
Ga ’Yan Real-Madrid
Gaisuwa ga ma’aikatan Aminiya da makarantanta, wadanda suka hada da masoyiyata Ummul-Khaeery da ’yan uwanta da ’yan uwana ’yan real-madrid. Daga Musa Na Musa PZ 08156572079.
 
Ga Gwamnan Kano
Salam. Editan Aminiya ka tambaya mana Gwamnan Kano, wai me ‘yan kasuwa suka yi masa, har yake son kashe kasuwanci a Kano. Duk hanyar da ’yan kasuwa za su zo sayayya ya rushe ta. Daga Sunusi Musa Ciyaman Kasuwar Singa Kano 08020800420.
 
Irinku PDP take so
Assalamu alaikum Edita, sauyin shekar Shekarau ba mu yi mamaki ba. Don ka taba yin abin da ya fi wannan, Buhari ya daga hannunka ya ce mu zabe ka, ba mu san da kai ba, muka ce an gan ka, amma daga baya ka ce farin jininka ne ya kai ka. To dama irinku PDP take so. Daga TEEMAH  BABY Fagge 07034888424.
 
Ina ra’ayin Shekarau?
A Kano kowa yana fadin albarkacin bakinsa a kan dakatarwar da aka yi wa Sanusi Lamido Sanusi, kai ka yi shiru. Shin kana goyon baya ko kuwa a’a. ’Yan Kano suna ta sauraren naka ra’ayin. Ko don kana kwadayin mulki a PDP ne? Daga Muhammad Nazifi a Kano 07038752013.
 Addu’a ga Najeriya
‘Yan Najeriya mu ci gaba da addu’a. Allah Ya zaunar da kasarmu lafiya./ Daga Sani Abdu Beta 08178112034.