✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid za ta sayar da Toni Kross da Ronaldo don sayo Neymar

Rahoton da kafar watsa labaran wasanni a Sifen Don Balon ta kalato an nuna kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin sayar…

Rahoton da kafar watsa labaran wasanni a Sifen Don Balon ta kalato an nuna kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin sayar da ’yan kwallonsa Toni Kroos da Cristiano Ronaldo a karshen kakar wasa ta bana don samun sukunin sayo dan kwallon PSG Neymar.

Manchester United dai ta nuna sha’awarta a kanToni Kroos yayin da Ronaldo ya nuna sha’awar barin Madrid a karshen kakar wasa ta bana kuma ya umarci dillalansa su tuntubi kulob din PSG na Faransa ko na Manchester United na Ingila a yunkurin canza shekarsa zuwa daya daga cikinsu.