Rahoton da kafar watsa labaran wasanni a Sifen Don Balon ta kalato an nuna kulob din Real Madrid da ke Sifen ya fara tunanin sayar da ’yan kwallonsa Toni Kroos da Cristiano Ronaldo a karshen kakar wasa ta bana don samun sukunin sayo dan kwallon PSG Neymar.
Manchester United dai ta nuna sha’awarta a kanToni Kroos yayin da Ronaldo ya nuna sha’awar barin Madrid a karshen kakar wasa ta bana kuma ya umarci dillalansa su tuntubi kulob din PSG na Faransa ko na Manchester United na Ingila a yunkurin canza shekarsa zuwa daya daga cikinsu.