✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madrid ta fara yunkurin dauke Juan Mata

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun nuna akwai yiwuwar dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United Juan Mata ya koma kulob din Real…

Rahotanni da ke fitowa daga Sifen sun nuna akwai yiwuwar dan kwallon tsakiya a kulob din Manchester United Juan Mata ya koma kulob din Real Madrid na Sifen.

Juan Mata wanda har yanzu ba ya buga wasa a kan kari a kulob din Manchester, akwai yiwuwar ya amince da tayin da Madrid din za ta yi masa.

dan kwallon wanda ya taba bugawa kulob din balencia da kuma na Chelsea yana fuskantar kalubale a kulob din Manchester, don rabonsa da yi wa kulob din wasa tun ranar da kulob din Huddersfield ya lallasa na United da ci 2-1 a gasar rukunin firimiyar Ingila.

Sai dai dan kwallon ya fara shakkar komawa Madrid don a ganinsa da wuya ne ya rika samun buga kwallo a kan kari ko da ya koma can ganin yadda kulob din yake da zaratan ’yan wasa.

Real Madrid dai tana fuskantar matsala a kakar wasa ta bana, don kawo yanzu kulob din FC Barcelona ya ba na kulob din tazarar maki 8 a gasar La-Liga ta Sifen a bana. Hakan ce ta sa kulob din yake kokarin cefano zaratan ’yan wasan da za su taimaki kulob din wajen fita daga cikin wannan matsala.