✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madara mai gyara fata

Yawan shan madara na kara lafiyar jiki. Tana gyara fata, ta sanya ta taushi da kuma santsi. Hakan ya sanya muka kawo muku yadda ya…

ZumaYawan shan madara na kara lafiyar jiki. Tana gyara fata, ta sanya ta taushi da kuma santsi. Hakan ya sanya muka kawo muku yadda ya kamata ku yi amfani da madara wajen gyaran fata.
·         Madara na goge daudar fuskar: A samu madara rabin kofi, sannan a hada ta da rabin cokalin gishiri, sai a sanya ruwa a gauraya har sai gishirin ya narke. Bayan hakan, sai a shafa a fuska da wuya zuwa minti 2 ko 3 kafin a wanke da ruwan dumi.
·         Madara na sanya fata santsi, don haka za a iya amfani da ita matsayin sinadarin ‘cleanser’. Da farko a samu auduga, sai a tsoma a cikin madarar ruwa, daga nan a rika goge fuskar da ita. Daga nan a jira ta bushe kafin a wanke.  Yin hakan na rage maikon fuska kuma zai sanya fuska ta yi taushi da santsi.
·         Za a iya amfani da madara don kara wa gashi karfi, musamman lokacin sanyi da gashi yakan tsinke. A zuba madara a kan gashi a cuda har ta taba tsagun kai, sai a jira na minti kadan kafin a wanke. Yin hakan na kara karfin gashi kuma yana hana shi tsinkewa.
·         Za a iya hada madara da zuma sannan a shafa a fuska. Yin haka na hana tsagewar fatar fuska saboda sanyi.