✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Madalla da datttijo Sa’idu Bala

Ma`abotan jaridun Kamfanin Media Trust, wato ta kullum-kullum da ta karshen mako da ta Lahadi-Lahadi, tsakanin watan Disambar bara zuwa Asabar din makon, da kanwarsu…

Ma`abotan jaridun Kamfanin Media Trust, wato ta kullum-kullum da ta karshen mako da ta Lahadi-Lahadi, tsakanin watan Disambar bara zuwa Asabar din makon, da kanwarsu ta makon jiya, watakila ya karanta labarin Likitocinnan mata hudu`ya`yan mutum daya da kuma na mahaifinsu, wadanda daya bayan daya suka bayar da labarin yadda suka yi karatun Likita, sannan zuwa yanzu kowaccensu ta kammala karatun zama kwararra a fannoni daban-daban.

Jaridar Daily Trust ta fara kawo wa mai karatu tarihin rayuwa da karatun Dokta Sa`adatu Bala, wadda ita ce babba a cikin jerin `ya`yan Alhaji Sa`idu Bala, wadda ita ta fara karatun aikin Likitin daga karfafa gwiwar mahaifinsu, Dokta Sa`adatu, ta yi karatun aikin Likitanta ne a Jami`ar Sakkwato, wadda a yau ake kira Jami`ar Usman danfodiyo, bayan da ta kammala karatunta na Sakandare ta `yan Mishan da ke Kano wato St Lious. Yanzu maganar da ake ita ce Darakta Janar ta Hukumar yaki da cutar kanjamau wato HIb/AIDS, kuma tana karatun digirin digirgir akan fannin Kiwon lafiyar al`umma a jami`ar Western Cape ta kasar Afirka ta Kudu. Tana da `ya`ya uku da jikoki biyu.
Sakon Dokta Dokta Sa`adatu, ita ce Dokta Rakiya Sa`idu, babbar Malama ce a asibitin Koyarwa na Jami`ar Ilorin, kuma kwararriya a fannin cututtukan matuncin mata, a halin yanzu tana karatunta na digirin digirgir akan wannan fanni da Jami`ar Cape Town ita ma a kasar ta Afirka ta Kudu, tana da aure da `ya`ya hudu. Sai Dokta Hadizah, wadda ita kuma kwararriya ce akan fannin cututtukan zuciya, tana kuma aiki da Asibitin kwararru na Murtala da ke birnin Kano, baya ga aikin koyarwa da take yi wa masu koyon aikin Likita na Asibitin Koyarwa na Malam Aminu da ke Kano, ita ma tana da aure da `ya`ya. Yar autar mata a wannan jerin ita ce Dokta A`isha, da ta kammala karatun aikin Likita a shekarar 2004, daga Jami`ar Bayero, yanzu kuma tana neman ta kware akan ilmin hoton sassan jikin dan Adam, fannin da ta ce ta zaba bisa ga irin karancin mata da ake da su a cikinsa. Ita ma tana da aure, da `ya`ya biyu.
Wani abin sha`awa ga wadannan mata, shi ne, a yanzu a kasar nan, babu wasu iyali da suke da `ya`ya mata kai har ma mazan, da suka haura biyu da suka karanci aikin Likita, kai ko mai uku babu bare hudu, sai daga iyalin Alhaji Sa`idun. Dadin-dadawa a hirar da aka yi da Likitocin gidan Alhaji Sa`dun, kowaccensu ta tabbatar da cewa taimako da karfafa gwiwar da ta samu daga mahaifinsu, shi ne jigon da ya sa ta jajirce ta kai ga nasarar zama Likita, duk kuwa da irin wahalar karatun da tsarabe-tsaraben da ke tattare da shi, dari-darin da mata ke yi na karatu da maza.
Abin tambaya a nan gagarumar nasara ta `ya`ya matan Alhaji Saidu Bala, haifaffen unguwar Jakara ta tsakiyar birnin Kano kuma dan shekaru 85, yau a duniya, wanda bayan kyamar karatun boko da ya taso ya gani ana yi a cikin al`ummarsa, musamman akan `ya`ya mata, (kyamar da har gobe ana fama da ita), ita ce ya ya ya yi nasara? Kafin jin amsar wannan tambaya, sai in ce mu yi nazarin tarihin dattijon arziki. Alhaji Sa`idu Bala haifaffen unguwar Jakara a Kano a shekarar 1928. Ya yi karatun Alkur`ani da karatun zaure. Bai fara koyon karatun boko ba, a cikin harshen Hausa ba sai a shekarar 1955, yana dan shekaru25, da haihuwa ke nan, albarkacin Alkura`ani ya koyi rubutun Hausar cikin shekara daya kacal. Neman ilmin addini ya kai shi garin Badun ta kudancin kasar nan da kuma kasar Ghana.
Bayan ya dawo daga Ghana ya samu shiga Makarantar koyon harshen Larabci ta SAS da ke Kano tsakanin shekarar 1959 zuwa 1963, ta hanyar amininsa Farfesa Shehu Galadanci, haka ya yi ta neman ilmi, bayan ya bar harkokin kasuwanci da ya fara har ya samu shekaru bakwai a cikinsa, amma ya zabi neman ilmi. Neman ilmin nan ya kai shi har Misira. Anan cikin gida kuma da karatu ya inganta har Jami`ar Bayero ya yi karatu. Ta fannin aikin koyar da addinin Islama Alhaji Sa`idu, ya yi aiki a Makarantar Alhassan dantata da ke unguwar koki ta cikin birnin Kano, daga nan ya koma aikin da gwamnati, inda ya rike mukamai daban-daban har zuwa lokacin da ya yi ritaya.
A bangaren siyasa, tun a jamhuriya ta farko Alhaji Sa`idu yake cikin jam`iyyar NEPU SAWABA, amma a jamhuriya ta biyu jam`iyyar NPN. A jamhurita uku da ba ta kai labari ba, wato 1991 zuwa 1993, Alhaji Sa`idu ya yi jam`iyyar NRC, inda har Gwamnan Kano na wancan lokacin, Sanata Kabiru Gaya ya yi masa mai bada shawara na musamman kan harkokin addini.
Mu dawo kan tambayar dalilin karfafa wa `ya`yansa mata har suka zama Likitoci. A fadarsa, fadi tashin da ya sha na neman ilmi da girmansa ya sanya ya yi alkawarin duk `ya`yansa sai sun yi karatun zamani. Amintakarsa da sa`o`insa irinsu tsohon Al`kalin Alkalan Jihar Kano marigayi Dokta Hassan Gwarzo da Farfesa Shehu Galadanci, da suka yi boko, suka kuma sanya `ya`yansu maza da mata har wasu suka yi karatun Likita, ita ta karfafa masa gwiwar ganin `ya`yansa sun zama Likitoci. Ya sha kalubalen kan `ya`yan nasa musamman mata da suke manya akan kar su yi karatun zamanin, tun daga kan mahaifiyarsa da ta nuna kwadayin su yi aure, amma dai ya daure ya sa su, abinda ya ce a yau yana haifar mai jin dadi da godiya ga Allah.
Sannu a hankali ana kara samun wayewar kai na al`ummar Hausa/Fulani akan tura `ya`yansu, makaratun boko musamman mata, amma har yanzu al`ummarmu na baya akan wannan muhimmin fannin da ci gaban rayuwa gaban kaf ya rataya akansa wato ilmi kowane iri. Don haka ya kamata mu san cewa muna cikin karni na 21, duniya ta ci gaba, amma mu ana ta terere da mu akan mu ne koma baya kusan akan komai, don kawai mun ki rungumar zamani.